1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tsagaita wuta a Sudan ta Kudu ya ruguje

May 15, 2014

Ɓangarorin da ke gaba da juna a ƙasar sun ba da labarin gwabza faɗa da amfani da manyan bindigogin atileri a jihar Upper Nile mai arzikin man fetir.

https://p.dw.com/p/1C0vP
Konflikt im Südsudan Regierungssoldat 31.12.2013
Hoto: Samir Bol/AFP/Getty Images

Dakarun da ke yaƙi da juna a Sudan ta Kudu a wannan Alhamis sun gwabza ƙazamin faɗa sannan sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta. Hakan na zuwa ne daidai lokacin da yaƙin basasan ƙasar ya shiga watansa na shida yayin kuma ake gargaɗi game da fuskantar matsananciyar yunwa matuƙar aka ci gaba da zubar da jini. Dukkan ɓangarorin da ke gaba da juna sun ba da labarin gwabza mummunan fada da amfani da manyan bindigogin atileri a jihar Upper Nile mai arzikin man fetir. Yakin a cikin wannan jaririyar ƙasar ya yi sanadiyar rayukan dubun dubatan mutane inda sama da miliyan 1.3 aka tilasta musu tserewa daga gidajensu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane