1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tsagaita wuta a Siriya

April 4, 2012

Al'ummar kasa da kasa ta sanya ido ta gani ko shugaba Bashar al-Assad zai cika alkawarinsa na tsagaita wuta ran 10 ga watan Afrilu

https://p.dw.com/p/14XNw
epa03139216 A handout picture released by Syrian Arab News Agency SANA, shows Syrian President Bashar Al-Assad (R) listening to UN Arab League envoy Kofi Annan (L) during their meeting, at Syrian presidential palace in Damascus, Syria, 10 March 2012. Annan arrives in Damascus on 10 March and is expected to call for talks between the government and the opposition in a bid to end the year-long violence. EPA/SANA HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Kofi Annan da shugaba Bashar al-AssadHoto: picture-alliance/dpa

Majalisar Dinkin Duniya na jagorantar wani shirin sulhu a kasar Siriya, kamar yadda mai magana da yawun wakilin kasa da kasa a rikicin Siriyan wato Kofi Annan ya bayyana. Ana sa ran daga gobe, wata tawagar Majalisar zata isa birnin Damascus domin ta ga ko shugaba Bashar al-Assad zai cika alkawarinsa na janye dakaru daga ranar 10 ga watan Afrilu, ya kuma tsagaita wuta kamar yadda ya amince.

To sai dai ko da ma shugaba Bashar al-Assad ya gaza bada hadin kai wajen cimma wannan wa'adin 10 ga watan Afrilun da aka basa, wasu majiyoyin diplomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya sun ce Annan zai cigaba da neman taimakon kasashen Rasha da China wajen dakatar da rikicin na shekara guda yanzu.

Ran litinin ne manzon kasa da kasa, mai shiga tsakanin rikicin na Siriya Kofi Annan ya fadawa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya cewa ce a karon farko siriya ta yi alkawarin tsagaita wuta kuma ana sa ran kwamitin ya bada goyon bayansa ga wannan kuduri nan ba da dadewa ba.

Duk da cewa Rasha bata goyon bayan tsoma bakin kasashen ketare, ta goyi bayan wannan kuduri kuma ta yi kira ga Siriya da ta dauki matakin farko wajen tsagaita wuta. Ko da shike jam'an diplomasiyya sun ce da kyar ne Assad ya cika wannan alkawari.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal