Shirin tattaunawa tsakanin Rasha da Siriya
February 7, 2012Zuwan na minista na ƙasar ta Rasha kan ya biyo bayan hau kujerar na ƙi da ƙasashen Rasha da China suka yi a ƙarshen mako a taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinki Duniya ,wajan ɗaukar matakin yin allah wadai da kudirin da ya yi allah wadai da kisan gilar da gwamnatin Bashar Al Assad ta ke yi.
yanzu haka dai sojojin gwamnatin a siriya na ci gaba da fatatakar jama'a inda aka ƙiesta cewa sun kashe kusan mutane ɗari kawo yanzu.Tuni dai da ƙasashen Amurka da Ingila suka sanar da janye jami'an diflomasiyar su a ƙasar yayin da kuma ministan harkokin waje na ƙasar Jamus Guido Westerwelle ya ce ƙasar sa za ta bi sahun duk wani mataki da ƙawayenta na Turai suka ɗauka akan Siriya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu