1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin samar da zaman lafiya a Libya

Ramatu Garba Baba
September 14, 2017

A wannan Alhamis kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin doka da zai bai wa bangarorin da ke jajayya da juna a kasar Libya dama na zama tare don samar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/2k0bY
USA New York Sicherheitsrat der Vereinten Nationen über Libyen
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/L. Muzi

Kwamitin ya amince da kudurin dokar a wani zama da aka yi a wannan Alhamis inda aka amince da bai wa bangarorin da ke jajayya da juna goyon baya na zama tare don samar da zaman lafiya karkashin jagorancin kwamitin, a cewar babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen rikicin kasar ta Libya a kuma samar da zaman lafiya dawamaimiya.

Kwamitin ya yi na'am da Kudirin da kuma tsawaita zaman dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na tsawon shekara guda tare da bai wa bangarorin goyon bayan da suke bukata. Guguwar juyin juya hali ta kada a kasar Libya a shekara ta 2011 lamarin da ya kai ga hambarar da marigayi Mamman Ghadafi daga karagar mulki, tun wannan lokacin Libya ke fama da tashe tashen hankula sakamakon rikici a tsakanin bangaren gwamnati mai rikon kwarya dana  mayakan sa kai.