Shirin ya kunshi labaran duniya wanda a ciki aka ji cewa kasar Habasha ta soki lamirin Majalisar Dinkin Duniya na kakabawa Sudan ta Kudu takunkumi. Baya ga labarai, akwai shirin Afirka a Mako wanda kan yi bitar muhimman batutuwa da suka fi daukar hankali a nahiyarmu ta Afirka a wannan makon mai karewa.