1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: bukatar yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Mohammad Nasiru Awal AH
February 14, 2020

Mika tsohon shugaban kasar Sudan ga kotun ICC da batun daukar gagarumin mataki wajen yaki da ta'addanci a yanki Sahel da matakan riga kafi na hana shigar cutar Coronavirus a Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3Xmzk
Sudan Khartum | Prozess & Urteil Omar al-Baschir, ehemaliger Präsident
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Hajaj

 

Da farko jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi gwamnatin Sudan na da niyyar shiga tattaunawa da 'yan tawayen yankin Darfur sannan lokaci guda ta yanke shawarar mika tsohon shugaban mulkin kama karya Omar al-Bashir ga kotun duniya da ke The Hague. Jaridar ta ce a shekarar 2009 kotun ta ba da sammacin kame al-Bashir bisa zargin kisan kiyashi da aikata laifin yaki da cin zarafin dan Adam musamman a yankin Darfur yammacin kasar ta Sudan, amma ya musanta wannan zargi. Sai dai yanzu kofa ta bude ta gurfanar da shi gaban kotun. Jaridar ta ce an kuma samu ci-gaba a lokacin wani taro tsakanin gwamnatin rikon kwarya da kungiyoyin 'yan tawaye musamman na Darfur. Tun a bara aka fara maganar kawo karshen rikice-rikice a kasar, abin da ya kai su ga fara zaman tattaunawa a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu. Dan kama karya zai gurfana gaban kotu wannan shi ne taken labarin jaridar Der Tagesspiegel, wadda ta kara da ba hujjojin da suka sanya sojin Sudan za su mika al-Bashir. Ta ce ko shakka babu sojin Sudan sun dauki gagarumin mataki da ke nuni da sauyin tunanin hafsoshin sojin a kan batun al-Bashir da aka hambarar da gwamnatinsa cikin watan Afrilun shekarar 2019. Jaridar ta ce matakin na da nasaba da zaman tattauna batun zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyin tawaye da dama na yankin Darfur, kuma daya daga cikin buktaun 'yan tawayen shi ne a mika al-Bashir ga kotun ta ICC. Ko da yake ba a bayyana ranar da za a tasa keyarsa ba amma masharhanta na ganin sai bayan an kammala tattaunawar zaman lafiya.

Akwai bukatar daukar matakai na kirki wajen yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Frankreich l Macron wirbt für Sahel-Initiative - Soldaten in Mali
Hoto: picture alliance/dpa/K. Palitza

Ana bukatar gagarumin shiri a yaki da ta'adda a yankin Sahel, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhin da ta yi kan rikicin 'yan ta'adda a kasashen yankin Sahel. Ta ce ra'ayin masana a yankin ya zo daya cewa rikicin yankin na Sahel na barazanar kara tabarbarewa duk da kara yawan dakarun da Faransa ta yi. Jaridar ta kara da cewa kudurin da shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwarorin aikinsa na kasashen Burkina Faso, Mali, Mauritaniya, Nijar da Chadi da suka yi wani taro a garin Pau na kasar Faransa a ranar 13 ga watan Janeru da ya gabata, suka dauka na karfafa hadin kan ayyukan soji ba zai wadata a karya lagwan ayyukan ta'addancin da suka zama ruwan dare a yankin. Dole sai manyan kasashen duniya musamman na Turai sun ba da gagarumar gudunmawa tare da shiga gdan-gadan cikin lamarin, matukar ana son a ga bayan 'yan ta'adda a yankin. Wani muhimmin abu kuma shi ne a inganta halin rayuwar al'ummomin yanki a dukkan bangarori na rayuwa.

Nahiyar Afirka na kokarin daukar matakai hana shigar cutar Coronavirus a nahiyar

China Shanghai | Coronavirus | Produktion von Schutzmasken
Hoto: picture-alliance/dpa/Maxppp/Kyodo

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung da ta yi tsokaci kan matakan da kasashen Afirka ke dauka na hana cutar Coronavirus shiga nahiyar, tana mai cewa tun lokacin da aka yi fama da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango aka san yadda ake auna zafin jikin matafiya da ke sauka a filayen jirgin saman gabashin Afirka. Ta ce tun kafin a tambayi fasfo dinsu, ana bukatar matafiya su amsa tambayoyi inda suka fito, ko sun ziyarci Chaina cikin watanni biyu da suka wuce, ko suna da alamun zafin jiki ko tari?