1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a koma wasannin Lig a Spain da Ingila

Gazali Abdou Tasawa
May 25, 2020

Kasashen Ingila da Spain na shirye-shiryen komawa wasannin lig din kwallon kafa na kasashensu wato La Liga da Firimiya Lig wadanda aka tsaida makonni da dama a sakamakon annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3cjT8
Premier League | FC Liverpool - Sheffield United | Sadio Mane
Hoto: picture-alliance/Actionplus

Firimiya Lig:

Gwamnatin Birtaniya ta ba da izinin zuwa mataki na biyu na shirin fara wasannin kwallon kafa na Firimiya Lig bayan katse su sakamakon annobar Corona. Wannan yana nufin cewa daga wannan Litinin 'yan wasa na da damar yin atisaye kusa da kusa, kuma wannan zai kasance sharar fage na fatan komawa ga fafatawa a watan Yuni. A lokacin da yake tsokaci a kan wannan batu ministan wasanni, Nigel Huddleston ya ce ana yin wannan taka tsan-tsan din ne da nufin takaita hadarin rauni da kare lafiyar 'yan kwallo da ba duk masu ruwa da tsaki a gasar Firimiya Lig.
Ita dai gwamnati Birtaniya tana kokarin sake farfado da wasannin kwallon kafa ba tare da 'yan kallo ba, inda a ranar 18 ga Mayu ta fara ba da izinin yin atisaye tsakanin kananan rukunoni na 'yan wasa. Tuni dai shugaban Hukumar Tsara Gasar Firimiya Lig Richard Masters ya nuna karfin gwiwa game da burin da aka sa a gaba game da komawa fagen kwallon kafa a Ingila a watan Yuni, duk da barazanar da kasar ke fuskanta daga Coronavirus. Sai dai har yanzu ba a tantance ranar fara wasanni a Ingila ba. An fara ambato 12 ga Yuni a matsayin ranar dawowa wasannin na Firimiya Lig, kafin daga bisani hukumomi suka fi karkata a kan ranar 19 ga Yuni.

Fußball-Spieler Pierre-Emerick Aubameyang
Hoto: Getty Images/L. Parnaby

La Liga:
Kafofin watsa labaran kasar Spain sun nuna doki da murna kwanaki biyu bayan da Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ce za a ci gaba da gasar La Liga a ranar 8 ga watan Yuni ba tare da 'yan kallo ba. Sai dai a cikin sharhin da Jaridar Marca da ta fi samun karbuwa a kasar ta yi, ta ce babbar lig din Spain za ta kara fuskantar kalubale da yawa don tabbatar da ingantacciyar tafiyar kama daga na tsakanin zafi da za a ci karo da shi, har ya zuwa gudanar da wasanni ba tare da 'yan kallo ba, da kuma uwa-uba barazanar kiwon lafiya da annobar Corona ta haddasa.
Makonni 11 na karshe la Liga za su gudana ne a lokacin bazara, saboda haka ne a yayin ganawarsu tare da hukumomi a karshen mako, kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Spain ta nemi da a samar da lokacin shan ruwa kafin a koma wasa idan yanayin zafi ya kai tsakanin digiri 28 zuwa 32, kuma a jinkirta horarwa ta 'yan kwallo inda zafi ya wuce digiri 32. Sannan kuma kungiyar ta AFE ta nemi da a samar da tsarin hutu na tsawon awanni 72 a tsakanin wasanni biyu na kungiyar daya, lamarin da ya yi hannu riga da shawarar da hukumar kwallon kafar Spain da ta ce za a yi "wasan kwallon kafa a kullin yaumin.

Lionel Messi in Barcelona 2020
Hoto: Imago Images/AFLOSPORT