1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ceton Girka na gamuwa da tsaiko

February 15, 2012

Ministocin kudi na ƙasashen kungiyar Tarrayar Turai sun ɗage domin tattauna hanyoyin bayar da ƙarin tallafi ga ƙasar Girka har i zuwa nan gaba.

https://p.dw.com/p/143QG
Greek Prime Minister Lucas Papademos delivers a speech during the annual conference of the American-Hellenic Chamber of Commerce in Athens, Wednesday, Dec. 14, 2011. Greece's rescue creditors on Wednesday pressed the debt-shackled country to fire excess public servants and further scale back workers' pay rights. (Foto:Thanassis Stavrakis/AP/dapd)
Lucas Papademos fraministan GirkaHoto: dapd

Ministocin sun ce zasu tattauna ta waya talho a maimakon haduwar gaba da gaba saboda har yanzu a kwai sauran abubuwan da ba a daidai ta ba gabannin zaman taron.An shirya jagoran jam'iyyar masu raayin riƙau ɗaya daga cikin ƙawancce jam'iyyun siyasar da ke yin mulki Antonis Samaras.

Zai bada goyon bayan jam'iyar sa a rubuce ga hukumomin Girkan; dangane da sabbin matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin wanda ƙungiyar Tarrayar Turai ta buƙaci ƙasar ta aiwatar.Ƙungiyar ta Tarrayar Turai na buƙatar samun ƙarin tabbacen hukumomin Girkan na ƙaddamar da shirin wanda ake ci gaba da samun saɓannin ra'ayoyi tsakanin ƙawancen jam'iyyun siyasar dake yin mulki.A wannanan tallafi na biyu dai ƙasar ta Girka za ta sami kimanin biliyan dubu 130 na kuɗin Euro.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu