1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ceto kudin Euro ya shiga halin rashin tabbas

Halimatu AbbasSeptember 10, 2012

A ranar Laraba ne kotun tsarin mulkin Jamus ta ce za ta tsai da shawara akan asusun ceto kudin Euro da kuma tsarin kudi na babban bankin Turai. To sai dai wani dan majalisar dokokin Bundestag ya shigar da kara

https://p.dw.com/p/165vM
ARCHIV - Der CSU-Politiker Peter Gauweiler steht am 07.09.2011 im Bundesverfassungsgericht in Karlsruhe. Am kommenden Mittwoch (12.09.2012) verkündet das Bundesverfassungsgericht seine Entscheidung über den Beitritt Deutschlands zum Euro-Rettungsschirm ESM. Foto: Uli Deck dpa/lsw (zu dpa Themenpaket «Euro-Entscheidung» vom 09.09.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Peter Gauweiler ya shigar da karar gaggauwa a kotun da ke da mazauninta a birnin Karlsruhe game da halin rashin tabbas da za a fuskanta a dangane da haka Gauweiler ya ce wannan karar martani ne ga shawarar da babban bankin Turai ya tsayar ta rashin kayyade takardun basukan da zai saya daga kasashen Turai da ke fama da bashi. Dan majalisar ya ce yin hakan zai haifar da rudani wajen tsai da hukunci akan shirin ceto kudin Euro, zai kuma yi lahanin gaske ga kasafin kudin Jamus. Ya ce bankin na bukatar janye shirinsa na sayen takardun basukan.

Mawalafiya; Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala