1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin yaya za a lalata makamai masu guba na Siriya?

September 12, 2013

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce kasar na iya shiga cikin aikin lalata makamai masu guba na Siriya domin tana da fasaha yin wannan aiki.

https://p.dw.com/p/19geV
Employee wears gas masks and suits at the chemical air weapons destruction facility on the premises of a new chemical weapons destruction facility at the Settlement of Maradykovo, Kirov Region, on September 10, 2006. The facility's first construction stage has been completed lately. Foto: Grigory Sysoyev +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A daidai lokacin da kasashen duniya ke nuna goyon baya ga shawarar da kasar Rasha ta bayar cewa Siriya ta mika makamanta masu guba domin kaucewa daukar matakan soji a kanta, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce Jamus na iya shiga cikin aikin lalata makamai masu guba na Siriya, domin a cewarsa Jamus din na da fasaha da kuma kwarewa na yin wannan aiki.

Makamai masu guba na daga cikin munanan makaman yaki da ke iya janyo illa na dogon lokaci a yankunan da aka yi amfani da su.

A yake-yake an yi amfani da su ne domin haddasa babbar asara ko raunuka ko gurbata muhalli da lalata tsarin kiwon lafiyar abokan gaba, makamansu ko cin lagonsu.

Abubuwan da suka faru a lokacin yakin duniya na daya ya sa a shekarar 1925 aka kulla yarjejeniyar kasashen duniya da ta haramta amfani da makamai masu guba. Sai dai yarjejeniyar ta Geneva ba ta hana yin bincike, kerawa da kuma tara makamai masu guba ba. Sai bayan yakin cacar baka aka dauki karin mataki, inda a shekarar 1993 wata yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta haramta mallakar makamai masu guba, wadda kasashe 189 suka rattaba wa hannu.

Ein Soldat steht in der Fabrik Kambarka in der russischen Teilrepublik Udmurtien hinter technischen Einrichtungen einer Anlage zur Vernichtung von Chemiewaffen (Foto vom 01.03.2006). Russland nahm am 01.03.2006 in Kambarka die zweite mit deutscher Hilfe finanzierte Anlage zur Vernichtung von Chemiewaffen in Betrieb. Dort sollen bis April 2007 ca. 3000 Tonnen chemischer Kampfstoffe unschädlich gemacht werden, sagte Generalmajor Igor Kondakow, der stellvertretende Leiter der Militärbehörde für die Lagerung und Vernichtung von Chemiewaffen. Er schätzte die Gesamtkosten des Betriebes von Kambarka, das etwa 1300 Kilometer östlich von Moskau liegt, auf neun Milliarden Rubel (270 Millionen Euro). Davon trage Deutschland ein Drittel. Foto: Grigory Sysoyev +++(c) dpa - Report+++
Ma'aiakata a wata cibiyar lalata makamai masu guba a Rasha inda ake amfani da fasaha daga JamusHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanonin Jamus na da kwarewa

A cikin shekaru 68 tsakanin yarjejeniyoyin biyu kasashen duniya da dama sun mallaki miliyoyin makamai masu guba, kuma tun a shekarun 1990 aka fara lalata irin wadannan makamai tare da fasaha daga Jamus. Alal misali kamfanonin GEKA da Eisenmann a Jamus sun yi fice wajen samar da fasahar lalata makamai masu guba.

Uwe Neumann shi ne babban manejan kamfanin Eisenmann ya yi karin haske game da aikin lalata makamai masu guba.

"A takaice dai muna mafani da wani murhu mai zafin gaske da ya kai awo 1200 a sikelin auna zafi. Ana saka makaman masu guba a ciki sannan a hura iskar oxygen a barsu ciki na wani lokaci. Da haka ake lalata makaman."

Sai dai wani hayaki mai guba na saura a cikin makaman, wanda ake amfani da dubaru daban-daban na tsabtace hayakin.

Copyright liegt bei der Firma Eisenmann. Bildunterschrift: Uwe Neumann, Senior Manager bei der Firma Eisenmann in Böblingen
Uwe Neumann na kamfanin EisenmannHoto: Eisenmann

Matakai daki-daki na lalata makamai masu guba

Kafin kona makaman da ke zama matakin karshe na lalatasu, sai da farko an ware raba sinadaran da makaman, inji Ralf Trapp masani a kan makamai masu guba a cikin hira da tashar DW.

"Zaban fasahar lalata makama ya dogara da yawan makaman da yanayinsu da kuma nau'in gubar dake cikinsu. Da farko ana amfani da magunguna don kashe gubar da ke cikin makaman. Ko da yake bayan wannan ma makaman na tare da guba to amma ba za a iya amfani da su a matsayin makaman yaki ba. A karshe ana lalata su gaba daya."

Masanin ya kara da cewa hatta wannan aiki yana da hatsari, yana bukatar wata fasaha ta musamman da kuma lokaci.

A dangane da makaman Siriya kuwa masanan sun ba da shawara da amfani da fasahar kona makamai masu guba don lalata su. Domin da haka za a kammala aikin da sauri.

Ba a sani ba dai ko Siriyar za ta lalata makamanta masu guba. Amma har idan an kai ga wannan matsayi to fa fasahar lalata makaman tana da tsada. An dai kiyasta cewa kudin da za a kashe wajen lalata makaman zai ninka sau goma kudin da aka kashe wajen samar da su.

Mawallafa: Alexander Drechsel / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu