1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ko masu bore a Masar za su samu biyan bukata?

February 11, 2011

Bisa ga dukkan alamu dai tura ta kai bango dangane da zanga-zangar al'uma a Masar, inda ƙasashen duniya suka ji takaici bisa jawabin Mubarak

https://p.dw.com/p/10FIn
Shugaba Husni MubarakHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban kasar Masar Husni Mubarak ya cije, ya yi kememe ya ki sauka daga mulki. Wannan matakin na sa wani babban hatsari ne ga abunda ka iya faruwa nan gaba, kamar yadda Rainer Sollich ke cewa a wannan sharhin.

Duk wani hasashe, duk wata fata da aka yi jiran samu, a karshe ya zama karya. Husni Mubarak bai girgiza ba. Yanzu ya yi wa 'yan kasar ba'a, inda ya ce shi dai ba zai sauka daga mulki ba. Ko da yake a nan gaba komai na iya faruwa, amma dai yanzu sojojin kasar ne ke da wuka da nama, kan makomar kasar, kuma hakan shine zai kawo karshen lamarin koma da wace irin manufa sojin ke da ita.

Su kansu jami'an leken asirin Amirka na CIA sun sa tsammanin Mubarak zai sauka a jiya. Masu bore a fadin titunan kasar Masar sun zaci hakan zai faru. Fushin jama'ar Masar ya kai iya wuya. Wannan shugaban yana wasa da hankalin 'yan kasar cikin wani mummunan yanayi.

Mubarak ya ci gaba da makalewa kan madafun mulki. Ya mikawa mataimakinsa Umar Sulaiman wani bangaren ikon mulki. Ya yi magana kan batun kawo sauyi, ya yi ikirarin shi dan kishin kasa ne, wanda zai kawo daidaituwar al'amura. Wada nan duka abune da ya fi karfin a zuba masa ido. 'Yan kasar Masar sun gaji da matsanancin rayuwa da rashin adalci da kuma tozartawar siyasa. 'Yan kasar sun jajurci sai sun samu 'yancin walwala, da tsarin dimokradiyya mai inganci, kuma suna samun goyon baya daga kasashen Turai.

Makalewa kan mulkin da Mubarak ke ci gaba da yi, wata alama ce ta wani bangaren ruruta tashin hankali, daga wannan boren da ake yi. Hakan zai shiga wani yanayin da babu mahalukin da zai shawo kansa, abinda zai bude kofa ga juyin mulkin sojoji. Kawo yanzu dai fatan da masu zanga-zangar ke da shi da ga sojojin bai kai ga biyan bukata ba. Mubarak ya sha alwashin shi zai kawo daidaituwar al'amura, wannan furucin nasa kansa, wani mataki ne da ke kara tsunduma kasar cikin wani babban hatsari na tsaro, ga ita kanta kasar Masar da ma sauran kasashen yankin baki daya.

Mai sharhi: Rainer Sollich cikin fassarar daga Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal