1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ko Afirka ta samu nata 'yan Taliban

Usman ShehuJuly 3, 2012

A ƙasar Mali rusa hubbaren waliyai da masu kaifin kishin Islama suka yi yana shan suka daga faɗin duniya

https://p.dw.com/p/15QhX
EXCLUSIVE IMAGES A still from a video shows Islamist militants destroying an ancient shrine in Timbuktu on July 1, 2012. Islamist rebels in northern Mali smashed four more tombs of ancient Muslim saints in Timbuktu on July 1 as the International Criminal Court warned their campaign of destruction was a war crime. The hardline Islamists who seized control of Timbuktu along with the rest of northern Mali three months ago, consider the shrines to be idolatrous and have wrecked seven tombs in two days. They began their destruction of tombs on JUne 30, 2012, after UNESCO put Timbuktu on its list of endangered world heritage sites. AFP PHOTO (Photo credit should read STR/AFP/GettyImages)
Lokacin da yan tawayen Mali ke rusa wani hubbare a TimbuktuHoto: Getty Images

Wanna wani saƙone mai birkitarwa: Inda a aka samu labarin cewa yan tawaye masu kaifin kishin Islama sun ruguza ɗaukacin hubbare dake birni Timbuktu. Saƙon mai birkitarwane sabo da bawai kayan tarihin birnin kadai aka rusa ba, amma tarihin nahiryar ce baki daya. Wannan hujja ce mai ƙarfi da yakamata ƙasashen duniya su dauka na yaƙar hatsarin yan ta'adda. Babbar Editar tashar DW Ute Schaeffer ta rubata sharhi a kai.

Wata alamace ta yin gargadi, inda Yan tsagerun na ƙungiyar Ansar Din suka yi amfani da diga da wuta wajen rusa hobberen waliyan da aka tinƙaho da su a birnin Timbuktu. Gargaɗin ba mai wani ƙarfi ba, kuma an nufe shi ne da ƙasashen yamma, amma kuwa zai tasiri kan tarihi da al'adun yankin, kamar yadda duniya ta son Timbuktu a matsayin ƙasar da ke da soraye tun daduruwan shekaru. Bayan kammala ɗanyan aikin nasu wani mai iƙararin shine kakakin ƙungiyar, Sanda ul Boumana yace sun gama ruguza hubbare 16 na waliye da kuma wadan ke a manyan masallatai uku na birni mai ɗaɗɗen tarihi wato timbuktu, daga nan tsagran sai yayi kabbara.

Ancient manuscripts dated from the 15th century are pictured in Timbuktu, Mali in October 2009. Timbuktu, Mali’s historic city and the legendary UNESCO World Heritage Site, is home to nearly 100,000 ancient manuscripts, some dating back to the Golden Age of the 12th and 15th centuries, written in Arabic or Africanized versions of the Arabic alphabets, and preserved in family homes and private libraries under the care of religious scholars. Citizens of Timbuktu attach great value to the books for their magical power of protection and healing. They are rallying to protect the ancient documents that officials fear may be looted or trafficked under the current occupation by Tuareg groups. Photo by Jean-Marie Hosatte/ABACAPRESS.COM # 322027_016
Litattafan tarhi dake cikin hatsari a TimbuktuHoto: picture-alliance/abaca

Kamar a Afganistan

Tun shekara ta 1988 birnin Timbuktu ya kasance a jirin biranen duniya na tari dake ƙarƙashin hukumar kula da al'adu ta MDD wato UNESCO. Kana tun a makwanni wannan hukumar ta UNESCO ta fara yin gargadi bisa hatsarin da kayan tarhi a Timbuktu ke fiskanta. Su dai wadanna yan tawaye Abzinawa dake kaifin kishin Islama daka sani da Ansaru Din abinda suka aikata dai yake da wanda ƙunguiyar Taliban ta yi a Afganistan, wadanda suka rusa wani wurin Ibadan Budda, halayen iri dayane, aƙidodjin dayane kuma yadda aka yi rushe rushen ɗayane.

Bayan da sojin Amirka suka mamaye Afganistan suka fara farautar yan Alƙa'ida, sannu a hankali yan ƙungiyar suka fara ƙaura izuwa yakin Sahel. ƙungiyoyin biyu da suka fara aikin ta'andancin tun shekaru masu yawa, sun kafu a waɗannan nahiyoyi dake da aksarin jama'arsu musulmai ne. Kai a yanzu mutun zai iya cewa sun mamaye duniya baki ɗaya.

Militiaman from the Ansar Dine Islamic group, who said they had come from Niger and Mauritania, ride on a vehicle at Kidal in northeastern Mali, June 16, 2012. The leader of the Ansar Dine Islamic group in northern Mali has rejected any form of independence of the northern half of the country and has vowed to pursue plans to impose sharia law throughout the West African nation. Iyad Ag Ghali's stance could further deepen the rift between his group and the separatist Tuareg rebels of the National Movement for the Liberation of Azawad (MNLA) as both vie for the control of the desert region. Picture taken June 16, 2012. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT RELIGION TPX IMAGES OF THE DAY)
Yan tawayen arewacin MaliHoto: Reuters

Alƙa'ida ta kafu a Afirka

A ƙasar Yamen da da ƙasashen Sahel, Alka'ida na iya laɓewa tana horar da mabiyanta. Daga nanan ake ƙinƙeshe sojojin ƙungiyar kana a aikasu sauran sassa na nahiyar. Wannan matkin wata dabare ce ta rikita nahiyar Afirka baki daya. Lamrin ya aurayane, da gwamnatocin mafa ƙarfin iko, da ƙungiyoyi masu aikata laifi da kuma, da rashin cibiyoyi masu ƙarfi, kana uwa uba tsagerun ƙungiyoyin dake da kaifin kishin Islama. Wadannan sune suka haifar da Alƙa'ida a Afirka. Dahaka suka kafa wata jinka wanda ta kaiga wurare irinsu Arewacin Najeriya. Annan yanzu ƙungiyoyin yan ta'adda dake Turai suna komawa Afirka.

Rikicin addini a Najeriya

Tun lokacin da aka fahimci irin wannan hada kai da, tsakanin kungiyoyin babu wanda zai rane ƙarfin da suke da shi. Ƙungiyar Boko Haram a Najeriyata sha daukar alhakin kai hare hare mujami'in ƙasar, tun jimawa aka fara cewa wannan ba danyen aiki yan ƙasa bane kawai, don haka wasu ke ganin cewa suna samun tallafi daga waje. Ita dai ƙungiyar Alƙa'ida ana zaton cewa tana samun kudinta daga fansar sace mutane, da sayar da muggan ƙwayoyi da kuma safarar makamai, kudin da take samu daga wadannan hanyoyin tana rabawa ƙungiyoyi dake ƙarƙashinta a fadin duniya.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Imam Abubakar Shekau, jagoran ƙungiyar Boko HaramHoto: AP

Lamarin ya fi ƙarfi mahukuntan yankin

Dole ƙasashen Turai da Amirka su fito a fili. Sojan ƙasar Mali su kadai ba za su iya yaƙar yan tawaye da mayaƙan Islama dake arewacin ƙasar ba. Suma ƙasashe maƙobta da Mali ba za su iya kawar da yan ta'adda a ƙasar ba. Misali Mauriteniya dake iyaka da Mali ta yamma ta sha fama da juyin Mulkin soji, haka ita Jamhuriyar Nijar da ke iyaka da Mali ta gashi, gwamantocin ƙasashen basu basu jima kan mulki da za su iya yin wani abun azo a gani. Don haka mafita itace, matakin ƙasar Amirka da Faransa wanda ta rani Mali, wannan shine kada ya saura, dole Turai duk da rikicin kudi da take fama da shi, amma ta yi hobbasa don kawo ƙarshen rikicin Mali.

Mawallafa: Ute Schaeffer / Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu