1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ina kasashen Sudan da Mali suka dosa?

May 7, 2012

Sudan da Mali da farautar shugaban LRA Joseph Kony sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/14rFK
Hoto: Reuters

Jaridun na Jamus a wannan mako sun duba al'amura da dama, cikin su har da halin da ake ciki a Sudan da rikicin kasar Mali da farautar shugaban mayakan kungiyar LRA na kasar Uganda, wato Joseph Kony, wanda duniya gaba daya take neman sa, kuma ake kyautata zaton yanzu haka yake da mafaka a kasar Sudan.

Kasashe biyu makwabtan juna, wato Sudan ta arewa da Sudan ta kudu, yanzu haka dai suna cikin hali ne na zaman doya da manja, koma ace zaman yaki tsakanin su. dalilin haka shie neman mallakar wani yanki na iyakar su, mai arzikinman fetur. Tun bayan da Sudan ta kuduj ta sami mukin kanta a bara, take neman mamaye wannan yanki da ake takaddama a kansa. Ya zuwa yanzu, mutane da yawa suka rasa rayukan su saikamakon dauki ba dadi tsakanin mayakan kasashen biyu. Hakan ya kai ga zaman taron musmman na kwamiktin sulhun majalisar dinkin duniya, tareda yiwa kasashen na Sudan guda biyu barazanar takunkumi, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta nunar a sharhin ta. Jaridar tace kwamitin sulhun ya tunatar masu da fanni na bakwai na kundin tsarin majalisar dinkin duniya, wanda ya tanadi dorawa kasashen takunkumi ko tura sojojin kwantar da rikici, idan har suka ki dakatar da gaba a tsakanin su. Kudirin ya kuma nemi SUdan ta kudu da Sudan ta arewa su gaggauta janye sojojin su zuwa iyakokin da duniya ta amince dasu.

Ita kuwa jaridar Tageszeitung ta duba haln da ake ciki ne a kasar Mali, inda tace zaman lafiya ya karewa wadanda suka aiwatarda juyin mulkin farko a wnanan kasa. Dalilin hakan shine kokarin jkuyin mulkin da wasu sojojin suka so yiwa takwarorin su dake kan mulki ranar Litinin, inda tun daga ran nan zuwa yanzu mutane masu tarin yawea suka mutu a fadan da ya biyo baya. Jaridar Tageszeitung tace kokarin juyin mulkin na farkonwnanan mako, ya kara jefa gwmanatin rikon kwarya ta kasarf cikin rudami, a kokarin ta na shirya sabon zabe tsakanin kwanaki 40, kamaryadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar, bisa manufarf sake maida ita karkashin tafarkin democradiya. Ko da shike tun farko aka gane cewar wannan wa'adi ma babu mai iya cika shi, amma a yanzu zai zama tilas an kara sabnon lokaci mai tsawo kafin gudanar da zaben. Kokarin juyin mulkin kuma, ya kara haddasa rashin tabbas a game dda yadda za'a shawo kan rikichin yan tawayen arewacin Mali, inda yan kungiyar MNLA suka kafa, suka kuma baiwa kansu mulkin kai karkashin jamhuriyarda suka kira, Azzawad.

Kämpfe in Mali Mai 2012
Rikici tsakanin sojoji a kasar MaliHoto: Reuters

Jaruidar Neues Deutschland kuwa a wnanan mako, ta duba farautar da ake yiwa shugaban kungiyar yan tawayen kasar Uganda ne, wato Joseph Kony, mutumin da ake zargin sa da aikata munanan laifukan yakida aiyukan rashin imani a kasar ta Ugandada makwabtan kasashe. A bayan da aka shiga farautar sa ta yanar-gizo, wato INternet, sojojin Amerika ma suna bada gudummuwa a game da neman sa. Masajna sun yi imanin cewar Kony bai yi nisa da mahaifar sa ba, domin kuwa ana zaton yanzuhaka ya sami maboyane a kasar Sudan. Ko da shike jakadan Sudan din a London ya musunta haka, to sai hakan ya biyo bayan amsa umurnine daga gwamnatin sa a Khartoum. Jaridar Neues Deutschland tace tuni dama kotun shari'ar masu aikata manyan laifukan yaki dake birnin Hague,ta bada sammacin kamo shugaban Sudan, Omar al-Bashirinda zai amsa tuhuma kan zargin kisan kare dangi. Idan kuwa har ya baiwa Kony mafaka, hakan zai kara iza wutar neman a gurfanar dashi gaban kotun sabnoda taimakawa kisan kare dangi.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita:Mouhamadou Awal