1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 3o na mulkin jam'iyyar MPS a Chadi

Dariustone Blaise
March 11, 2020

Jam'iyyar MPS na bukuwan cika shekaru 30 kan madafan iko a kasar Chadi, an yi bukukuwan ne na wannan shekarar a grin Mongo da ke ciki Lardin Guera a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3ZDGP
Tschad Idriss Deby
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Idan har tarihi ya nuna da 'yan kasar Chadi sun jin jinawa jam'iyyar da ke mulki ta Mouvement Patriotique du Salut (MPS) a takaice a shekarar 1990 biyo bayan korar tsohon shugaban kasar kuma dan mulkin danniya Hissène Habré.

A yanzu batun ba haka yake ba a zukata da bakunan da dama 'yan kasar Chadi, Amina wata matashiya ce da ba ta wuce shekaru 30 ba da haihuwa ta ce duk a tsawon rayuwarta ba ta san wani mulkin ba in bancin na jam'iyyar ta Idriss Daby MPS.

"A ina daga cikin dimbin matasan Chadi da ke ci gba da zaman kashe wando a gida bayan mun kammala karatu, wannan kuwa duk ta dalilin rashin iya kyakyawan jagorancin jam'iyyar MPS ne mai mulkin kasar da ta shafe shekaru 30 kan madafan iko, ba wani mulkin da muka sani in bancin wannan wannan abin bacin rai ne."

Haka abin yake a bakunan dimbin matasan kasar Chadi, wannan wani matashi ne mai suna Richard de Jésus, dan shekaru 22 cewa yayi.

"Ayar tambayar ita ce ko suna bukuwan kasawar da jam'iyyar ta yi na tsawon shekaru 30? Gwamnatin Idriss Deby ta kai makura domin komai ba za ta aiwatarswa ba, kamata ya yi Deby ya dauki mislin da takwaransa na kasar Cote d'ivoire Alassane Ouattara ko Issoufou Mouham,adou na Nijar da suka amince su bar mulki a hannun wasu sababin jini."

Suma dai jam'iyyun adawar kasar ba a barsu a baya ba wajen nuna rashin jin dadinsu da mulkin na shugaba Deby da jam'iyyarsa Succès Masra, wani matashin 'yan adawa ne da bai wuce shekaru shidda a duniya da Idriss Deby ya zo kan mulki ba, ya bayyana cewa kasar Chadi na bukatar sabon jini.

Tschad Straßenszene in Ndjamena
Cikin birnin NdjamenaHoto: DW/F. Quenum

"Kofa guda ce kawai ta fita ta rage mana ita ce ta shirya zaben da zai kawo gagarumin canji a kasar nan domin samar da wasu sababbin jini akan madafan iko kamar yadda kasar Chadi ke bukata. Ina kira ga wani tsari na tattaunawa domin samun mafita kan yadda 'yan kasar nan suka galabaita ta fannoni da dama kama daga fannin shari'a da na diyauta hakin dan Adam ga ko wane dan kasar."

Sai dai a cewar Abderamane Djasnabaye daya daga cikin kusoshin jam'iyyun da ke mulki batun ba haka yake ba.

"Batun kawo sauyi a tsarin tafiyar da mulki duk wani zance ne kawai,  mutane na maganar wa'adi biyu na mulki ka kalli Jamus masu mulkin kasar sun shafe wa'adi har sau hudu hakan kuma abin yake a sauran wasu kasashen na dabam, 'yan adawa su ne takamata su matsa kai mi domin ganin an kawo sauyi, ni dan demukuradiyya ne na fi amincewa da jama'a su fito don yin gwagwarmayar kwatar 'yanci, idan an matsa lamba don dorewar mulki shi ne ke haddasa matsala kalli abinda ke faruwa akasar Guinea duk rikicin na faruwa ne saboda batun wa'adi na biyu na mulki."

'Yan kasar Chadi da dama dai na ganin cewa batun kawo sauyi a tsarin tafiyar da mulkin kasar na a matsayin sai baba ta gani.