1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya: Biki ko jimami?

Ralf Bosen ZMA/LMJ
June 26, 2020

A ranar 26 ga watan Yunin shekara ta 1945 ne dai aka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa Majalisar Dinkin Duniya, a karshen taron majalisar da aka yi a birnin San Francisco na kasar Amirka.

https://p.dw.com/p/3eOmx
UN-Generalversammlung
Babban zauren Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Imago Images/Xinhua/Li Muzi

Yarjejeniyar dai ta fara aiki ne a ranar 24 ga watan Oktobar shekarar ta 1945 din, kuma dokar kafuwar kotun kasa da kasa, wani muhimmin sashi ne na wannan yarjejeniyar. Bayan sanya munanan abubuwan da suka faru a yakin duniya na biyu a bayansu ne dai, wakilan kasashe 50 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai a halin da ake ciki wadannan manufofi nasu na cikin wadi na tsaka mai wuya, duba da abubuwan da ke faruwa.

Akwai abin yi wa biki a bana?

Musamman da irin jawabai masu sarkakiya irin na shugaba Donald Trump na Amirka. Wanda wasu ke fassarawa da watsi da hukumomin kasa da kasa kai tsaye:"Idan kana son dimukuradiyya, to rike mulkinka. Idan kuma kana son zaman lafiya, ka so kasarka. Shugabanni masu hikima ko yaushe kan fifita al'ummarsu da kuma kasarsu fiye da komai. Makomar duniya ba ta hannun masana harkokin rayuwa, tana hannun masu kishin ƙasa. Makomar rayuwa tana hannun masu mulki da kasashe masu zaman kansu, wadanda suka dukufa wajen kare al'ummarsu, da daraja makwabtansu, da girmama dalilan da suka banbanta ko wace kasa ta zama ta musamman."

Hakan dai ya sake bayyana tsarin bai wa Amirkan fifiko ko da yaushe a zauren majalisar da ke New York, batun da ke bukatar gyara. Ga Trump dai manufofin Amirkan ne ke kan gaba, kafin duk wani batu na majalisar ya biyo baya.
Gabanin hawa kan karagar shugabanci a shekara ta 2016 dai, ta shafinsa na Tweeter Trump ya bayyana Majalisar Dinkin Duniyar a matsayin wani Klub da mutane ke haduwa domin yin nishadi. Shekara guda bayan nan, aka dauke ofishin jakadancin Amirka a Isra'ila da ga Tel Aviv zuwa birnin Kudus, batun da zauren majalisar ya yi Allah wada. Gunter Pleuger tsohon jakadan Jamus ne a zauren majalisar Dinkin Duniyar daga shekara ta 2002- 2006: "Da farko Tump ya gaza aiwatar da abubuwa da dama da ya dace a ce yana yi, musamman a bangaren bayar da muhimmiyar gudunmawa ga kwamitin sulhu na majalisar. Amma ba za a ce laifin Trump ba ne kacokan, har ma da  tsohuwar al'adar tafiyar da harkokin kwamitin sulhun shi kansa."
To sai dai duk da haka Majalisar Dinkin Duniyar ta cimma manyan manufofi da ke cikin yarjejeniyarta. Ranar 10 ga Disamba shekara ta 1948, aka cika yarjejeniyar da ta danganci kare 'yancin dan Adam. Kuma wannan wani muhimmin ci-gaba ne a tarihi, a cewar tsohon jakadan Jamus Hanns Heirich Schumacher. "Kama daga ci gaba da inganta 'yancin mata, zuwa 'yancin yara, da na masu bukata ta musamman, an samar da hukumomin da suka taka rawa wajen inganta 'yancin rukunin al'umma daban-daban a fadin duniya. Kada a manta da irin rawar da majalisar da jami'anta na musamman suke takawa a fannin ayyukan jin kai."

Syrien | WHO Polio Impfung
Amirka na janye tallafinta sannu a hankaliHoto: picture-alliance/dpa/ZUMAPRESS
UN-Generalversammlung in New York | US Präsident Donald Trump
Shugaba Donald Trupm na AmirkaHoto: AFP/S. Loeb

Barazanar Trump ta janye tallafi

Bayan haka Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi, ya ki shiga yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan 'yan gudun hijra, baya ga janye bangaren gudunmawar da kasarsa ke bayarwa a shirin wanzar da zaman lafiya. Amirkan har'ila yau ta fice daga Hukumar Bunkasa Ilimin da Raya Al'adu ta UNESCO da majalisar kare hakkin dan Adam.

A baya-baya nan shugaban na Amirkan ya ci zarafin Hukumar Kula da Lafiya ta majalisar WHO, inda ya yi zargin ta zama  'yar koren Chaina, tare da tsayar da ba da tallafi, a daidai lokacin da ake tsaka da ta'azzarar annobar cutar coronavirus cikin watan Mayu, kafin daga karshe ya sanar da raba gari da hukumar ta WHO.