1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Faransa ta cika shekaru 60

Abdoulaye Mamane Amadou
January 22, 2023

Albarkacin bikin cika shekaru 60 da kulla yarjejeniyar hulda, shugabannin Jamus da Faransa sun jaddada manufa guda kan ci gaban kasashen da ma nahiyar Turai baki daya

https://p.dw.com/p/4MYOr
60. Jubiläum des Élysée-Vertrags | Frankreich, Paris | Olaf Scholz und Emmanuel Macron
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Faransa da Jamus sun jadda matsaya guda na ci gaba da hulda tare domin ci gaban kasashen biyu da ma nahiyar Turai, albarkacin bikin cika shekaru 60 da saka hannu kan yarjejeniyar Elysse, da ta tanadi kyautata danganta a tsakanin kasahen biyu bayan yakin duniya na biyu.

Sugaban gwamnatin Jamus da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun halarci bukukuwan shekara-shekara na karrama yarjejeniyar a birnin Paris, a jawabinsa shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya jaddada goyon bayan kasashen biyu ga Ukraine da ke fuskantar mamaya daga Rasha, tare da ba ta duk tallafin da ta ke bukata.

Shugaba Macron ya ce lokaci ya yi na samar da wani sabon makamashi da karfafa wa sabbin fasahohin zamani, domin nahiyar Turai ta ci gaba da rike matsayinta ta fannoni da dama.

Shugabannin biyu za su jagoranci taron ministocin kasashen don tattauna batutuwa daban daban ciki har da na makamashi da tsaro da kuma tattalin arziki.