1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya: Tuni da kadawar guguwar juyin-juya-hali

Ramatu Garba Baba
January 13, 2023

Al'ummar kasar Tunisiya da dama ne suka gudanar da gangami domin tuni da ranar da guguwar juyin-juya-hali ta kada a kasar shekaru 12 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4M9Vs
Tunesien begeht Jahrestag der Revolution
Hoto: picture-alliance/dpa

Duk da kashedin da gwamnatin Tunisiya ta yi tare da kama masu fafutuka da wasu manyan 'yan jamiyyun siyasa, dubban dubatan 'yan kasar sun shirya gudanar da gangami domin tunawa da ranar da guguwar sauyin ta kada a kasar, shekaru goma sha biyu da suka gabata. Juyin- juya-halin ya kai ga kifar da mulkin kama karya na tsohon Shugaba Zine El Abidine Ben Ali.

Masu gangamin sun lashi takobin fara zanga-zangar ganin bayan mulkin Shugaba Kais Saeed, wanda suke cewa ba shi da wani banbanci da na Zine Abidine da 'yan kasar suka yi wa tawaye a baya. Tuni aka dauki mataki na tsaro inda aka baza jami'an 'yan sanda duk sassan kasar don kwantar da duk wata tarzoma da ka iya tasowa.