1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da katsalandan sojojin yamma Libiya

March 19, 2012

Ƙungiyar tsaro ta NATO ta tsoma baki a yaƙin na Libiya da sunan kare farar hula daga hare-haren dakarun Gadhafi.

https://p.dw.com/p/14N8j
An F-16 jet fighter flies over the NATO airbase in Aviano, Italy, Sunday, March 20, 2011. NATO's top decision-making body is set to decide whether the alliance will join in the strikes on Libya. Diplomats said NATO's military planners are due to present final action plans to the North Atlantic Council on Sunday. (Foto:Luca Bruno/AP/dapd)
NATO ta yi amfani da jiragen saman yaƙi don kai farmaki kan sojojin GadhafiHoto: dapd

A watan Janairun wancan shekara ne guguwar sauyi ta fara kaɗawa a ƙasashen Larabawa kama daga Tunisiya da Masar zuwa Aljeriya  inda mutane suka fantsama kan tituna suna neman komawa ga tafarkin dimukuradiya-abin da ya rutsa da gwamnatin shugabar Muammar Gadhafi na Libiya bayan da ya shafe shekaru sama da arbainin yana mulkin ƙasar.

Shi dai Muammar Gadhafi ya ɗauki matakin ba sani sabo domin murƙushe boren da aka tayar a birnin Bengazi na nuna adawa da gwamnatinsa inda mutane  da dama suka rasa rayukansu sakamakon yaduwar wannan bore a sauran yankunan kasar. Ba da jimawa ba ne dai  lamarin ya rincabe zuwa arangama tsakanin 'yan tawaye da magoya bayan Gadhafi har sai da ya kai inda  aka kafa gwamatin wucin gadi a gabashin ƙasar.

Ƙudurin MƊƊ kan rikicin ƙasar Libiya

Ganin haka ne yasa Majalisar Ɗinkin Duniya ta mai da martanin ta aza wa lIbiya takunkumin sayar da makamai. Bayan haka ne a ranar 17 ga watan Maris shekarar 2011 gamayyar ƙasa da ƙasa ta zartar da kudurin majalisar dinkin duniya na shekarar 1973 da ya ba da ikon daukar matakin soji domin ba da kariya  ga farar hula a Libiya. Kwanaki biyu kacal bayan zartar da wannan ƙuduri ne kuma  kasasnen Amurka da Birtaniya da Faransa suka haramci zirga zirgar jiragen sama da na ruwa akan Libiya   suka ka kuma fara yin luguden wuta akan sansanonin sojin kasar. 

A ranar 31 ga watan Maris ne sojojin kudunbala na kungiyar tsaro ta NATO suka dauki alhakin wannan aiki da ya kawo ƙarshe bayan watannin shida.  To sai dai an samu sakamako mai sarkakkiya daga wannan mataki kasancewar a hannu ɗaya hakan ya saɓa wa dokar da ta hana yin katsalanda a harkokin ƙasa mai cin gashin kanta a dayan hannun a baya ga sauyin  gwamnati 'yan tawayen sun kuma kashe  tsohon Shugaban kasar Muammar Gadhafi. Masu rajin kare hakkin bil Adama irinsu. Henning Rieke masanin siyasa na ƙungiyar dake nazari akan manufofin ketare a nan Jamus sun gano dacewar wannan mataki a matsayin abin da ka iya samar da mafita daga rkicin na libiya. To amma Rieke yace majalisar dinkin ta kai iyaka a aikinta na ba da taimakon jinƙai:

REFILE - ADDING TRANSLATION OF SIGNS People with the Kingdom of Libya flags and anti-federalization signs and banners gather during a protest against transforming Libya into a federal state, near the court building in Benghazi March 6, 2012. The signs read: "I'm from Benghazi. Al-Zubair Ahmed does not represent me" (L) and "We have one recognised Transitional Council. The Chancellor is the President". REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA- Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Libiya na fuskantar barazanar darewa bayan kashe GadhafiHoto: Reuters

"Ita dai Majalisar Dinkin Duniya ta kai ƙololuwar aikinta na ba da taimakon jinkai. Saboda cewa samar da sauyin gwammati a aikin da ta yi a Libiya  ya bakanta ran China da Rasha matuka ainun . Su dai wadannan kasashe  guda biyu sun dauki kudurin majalisar dinkin duniya akan Libiya a matsayin wani koma baya a gare su. A don haka ne ma suka hau kujerar na ki game da kudurin da komitin sulhu ke son dauka akan Siriya."

A dai ra'ayin Rolf Mützenich kakakin jamiyar SPD akan harkokin waje a majalisar dokoki ta Bundestag  matakin soji da aka dauka akan Libiya wani abu ne da ka iya mai da hannu agogo baya a  matakin kare fafar hukla nan gaba. 

Ɗaukar mataki na soji ba shine kadai ke  zai iya samar da mafita  ba. A mamaimakon haka kamata yayi a karfafa bin hanyon limana da dilomasiya domin samunmmafita daga riicin siriya.

Mawallafa: Sabine Hartert / Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal