1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AES ta cika shekara

Salissou Boukari SB
September 16, 2024

Shekara da kafa kungiyar AES da ta hada Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso wadda shugabannin uku suka saka hannu kan kundin gudanar da kungiyar ranar 16 ga watan Satumba da nufin hada karfi wajen yakar ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4kgZm
Mali, Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso lokacin taron hadin gwiwa
Shugabannin soja daga hagu zuwa dama: Kanar Assimi Goita na Mali, da Janar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar Nijar gami da Captain Ibrahim Traore na Burkina FasoHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Kare kai daga tsangwama ta manyan kasashen duniya sakamakon juyin mulkin da aka yi a wannan kasashe na yammacin Afirka. Albarkacin zagayowar ranar shugaban gamayyar kasashen kuma shugaban kasar Mali ya yi jawabi ga al'umomin kasashen uku inda ya kiran su ga bukatar hadin kai don cimma burin sabuwar tafiyar. A jawabin da ya yi wa yan kasashen uku na gamayyar kungiyar AES na Nijar Mali da Burkina Faso, shugaban kasar Mali wanda shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin Kanal Assimi Goita, ya ce shekara guda ke nan da kasashe uku suka dauki matakin da ya sauya tsarinsu na rayuwa da hulda ta zamantakewa a fannin tsaro da taimakekeniyar juna domin yakar ayyukan ta'attanci da duk wani tayar da zaune tsaye a yankin.

Karin Bayani: Shugaban Senegal zai sasanta ECOWAS da AES

'Yan Jamhuriyar Nijar
'Yan Jamhuriyar NijarHoto: AFP

A jawabin shugaban gamayyar kungiyar ta AES Kanal Assimi Goita, ya tabo batun yan kasashen na AES da ke zaune a kasashen waje inda ya jinjina musu kan taimakon da suke ba da wa don ci gaban yankin. Kasashen uku na Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkana Faso ta bakin shugaban kasar ta Mali sun sanar da shirin kaddamar da tsarin yada al'adu da motsa jiki gami da tsarin ilimi na hadin gwiwa nan ba da jimawa ba, domin karfafa hadin kan al'umomin kasashen da kuma shirin kirkiro wata kafar sadawa ta hadin gwiwa da za ta rinka ba da labarin kasashen cikin tsari da tsanaki don bai wa al'umma cikakken labari, inda aka yi kira ga dukannin al'umomin kasashen uku da su tashi tsaye don ganin an cimma wannan buri na mayar da yankin Sahel wata farfajiya da kowa zai yi sha'awar zuwa a cikinta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani