1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar samar da tudun mun tsira a Siriya

Gazali Abdou Tasawa
October 22, 2019

Ministar tsaron kasar Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta yi kira ga kasashen duniya kan samar da wani tudun mun tsira a arewacin kasar Siriya da zai zamo a karkashin kulawar kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/3RgEb
Annegret Kramp-Karrenbauer im Interview zu Sicherheitszone in Syrien
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ministar tsaron kasar ta Jamus kana shugabar Jam'iyyar CDU mai mulki, ta bayyana hakan ne a wata fira da tashar DW inda amma ta ce shirin na bukatar samun goyon bayan Turkiyya da Rasha.

 Ministar ta ce yankin da za a samar zai taimaka ga hana yaduwar ayyukan kungiyar 'yan ta'addar IS da kuma wanzar da zaman lafiya a yankin baki daya. Ministar ta kara da cewa majalisar dokokin kasar ta Jamus za ta yi nazari a game da yiwuwar aikawa da sojojin kasar a yankin.

 Makonni biyu da suka gabta ne dai rundunar sojin Turkiyya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawan yakin na Kungiyar YPG da nufin kwace yankin da ke hannunsu dan mayar da shi wani sabon matsugunnin miliyoyin 'yan Siriya da ke zaman gudun hijira a Turkiyya.