1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawara a kan farfaɗo da tattalin arzikin Girka

July 23, 2012

Ana yunƙurin taimaka wa ƙasar Girka domin farfaɗo da tattalin arzikinta da ya gurgunce sakamakon bashi.

https://p.dw.com/p/15dhC
Christine Lagarde, the Managing Director of the International Monetary Fund, addresses a press conference at the Treasury in London Tuesday May 22, 2012. The International Monetary Fund has issued a tough assessment of U.K. economic policy, urging the coalition government and Bank of England to do more to boost demand in the economy. (AP Photo Oli Scarff, Pool)
Hoto: AP

A ran Talatan nan ne, asusun bada lamuni na Majalisar Ɗunkin Duniya IMF zai ganawa da hukumomin ƙasar Girka domin nazarin tattalin arzikin ƙasar da ya faɗa cikin matsanancin hali sakamakon bashin da ya dabaibaye ƙasar tun shekara ta 2010.

A lokacin da ya ke magana a gaban manema labarai, wani kakakin asusun na IMF, ya ce sun tabbatar da ƙasar Girka na iya kokarinta na farfado da karfin tattalin arzikinta da ke cikin matsala,don haka za su yi zama na musamman da hukumomin ƙasar domin su duba hanyoyin warware wannan matsalar.

Mawallafi : Issoufou Mamane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar