1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Prozess gegen KAS in Ägypten

Usman ShehuJune 5, 2013

Ƙungiyoyi masu zaman kansu na fiskantar matsi a ƙasar Mansar tun bayan juyin -juya hali da aka yi a ƙasar.

https://p.dw.com/p/18k5G
epa03126612 A photo made available on 29 February 2012, shows judge Mohammed Shukri (L) presiding over the first trial session of defendants accused of working for unlicensed non-governmental organizations (NGOs) and receiving illegal foreign funds, in Cairo, Egypt, 26 February 2012. According to media reports on 29 February, Shukri made a formal request to renounce the case without citing a reason. Local media citing unnamed sources said his decision was made after Egyptian authorities reportedly asked him to drop a travel ban imposed on the 43 activists, including 19 Americans and two Germans, involved in the case. The proposed trial had caused a rift between Egypt and Western powers backing some of the NGOs. EPA/MOHAMED OMAR
Mohammed Shukri, alƙalin ƙasar Masar a zauren kotuHoto: picture-alliance/dpa

Juyin-juya halin ƙasashen Larabawa ya kawo sau yi mai yawa, misali a ƙasar Masar, bawai ga shugaban kama karya Husni Mubarak kaɗai lamarin ya rutsa da shi ba, amma a yanzu su ma ƙungiyoyi masu zaman kansu daga ƙasashen ƙetare lamarin ya shafe su, kai harma da wasu ƙungiyoyin da ke cikin ƙasar ta Masar, daga cikin ƙungiyoyin ƙasashen waje da lamarin ya shafa harda ƙidauniyar Konrad Adenauer.

Kamar yadda hujjojin da Aƙalin ya fitar, idan har an samu laifin da ake tuhumar ƙungiyoyin da akaitawa, to kuwa wasu ma'aikatan ƙidauniyar Konrad Adenauer su biyu, suna iya fiskanatar ɗauri a gidan yari na 'yan shekaru. Watanni takwasne dai bayan kifar da gwamnatin Husni Mubarak, wasu 'yan sanda suka kutsa cikin ofishin ƙidauniyar Konrad Adenauer, inda suka ɗauke na'urorin aiki da suka hada da kwampitoci, kana suka yi awun gaba da shugaban ma'aikatan ƙungiyar da ke birnin Alƙahira, ida bayan sa'o'i suka sako shi. Kafin a baiwa mutanen beli da kuma izinin tafiye tafiye, sanda suka ajeyi Euro dubu ɗari biyar. Hans-Gert Pöttering shine jagoran ƙidauniyar ta Konrad Adenauer, kuma DW ta tambaye shi, ko yaya suke kallon wannan shari'ar da hukumomi a Alƙahira suka gabatar.

Hans-Gert Pöttering, Vorsitzender der Konrad-Adenauer-Stiftung, spricht am Donnerstag (08.09.2011) in Berlin zum "Tag der Konrad-Adenauer-Stiftung". Die Veranstaltung stand unter dem Motto "Vielfalt erleben - Integration gestalten: In Deutschland zu Hause". Foto: Soeren Stache dpa/lbn +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hans-Gert Pöttering, shugaban ƙidauniyar Kondrad AdenauerHoto: picture-alliance/dpa

"Wannan shari'ar dai ba ta da ƙa'ida , mu tun fara shari'ar muke hangen wannan. Domin tuhumar da ake yi wa ma'aikatan mu a Alƙahira mun fahimci hakan. Kekkewan ayyukan da muka gudanar tsawon shekaru 30, tare da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasar, bai yi wani tasiriba a idanun wadannan alƙalan. Mun kaɗu sosai kan abinda ke faruwa a Alƙahira"

Shi dai alƙalin da ya jagoranci shari'ar bai fayyece ainihin dalilin kame wadannan ƙungiyoyi ba. Musamman wanda ya kai ga cin tara, inda misali tsohon jagoran ƙidainiyar Konrad Adenauer Andreas Jakobs an yanke mi shi hukuncin ɗaurin shekaru biyar da kuma tara. Peter Steffe shine wakilin ARD dake birnin Aƙahira, kuma yana bin diddigin shari'ar ga abinda yace.

"Mai gabatar da ƙara na gwamnatin Masar yace wai ana zargin ma'aikatan waɗannan ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa da laifin kasancewa cikin ƙasar Masar ba bisa izini ba, kuma suna shigowa da haramtattun kuɗi a cikin ƙasar"

Politische Partizipation Indigene in Lateinamerika Treffen_ Sumami2 Edgar Sumami, Jungpolitiker aus Bolivien, bei einem Treffen mit indigenen Familien. Santa Cruz de la Sierra, Bolivien. 2012. Autor/Copyright: Geraldine Domínquez. Politik, Partizipation, Indigene, Lateinamerika, Konrad Adenauer Stiftung, KAS, Regionalprogramm “Politische Partizipation Indígena- PPI “, Entwicklungsstrategie, Jungpolitiker, Fortbildung, Bolivien, Demokratien, Führungspersonen, Armutsbekämpfung, Völker, Kooperation, Edgar Sumami, Treffen, eingeborene
Jami'an ƙidauniyar Konrad Adenauer, a fagen aikin fadakar da jama'aHoto: Geraldine Domínquez

Akwai dai wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu daga ƙasar Amirka da wannan batun ya shafa, baya ga ƙidauniyar Konrad Adenauer ta ƙasar Jamus, kuma wannan hukuncin da gwamnatin Masar ta yi wa ƙungiyoyin na ƙasa da ƙasa, ya fara shafar ƙunguiyoyi masu zaman kansu na cikin gida, domin kuwa dama can sun dogara da tallafi da suke samu daga abokanen aikinsu daga ƙasashen ƙetare. To shin ko wannan abinda ya faru a Masar zai kassara ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu irin na Konrad Adenauer a wasu ƙasashen?. Ga dai jagoran ƙidauniyar amsar da ya bayar.

"Bana fatan hakan, amma dai yanzu mun zuba ido. Mu a matsayin ƙidauniyar Konrad Adenauer, muna ganin taimakon rayar ƙasashe musamman ga ƙungiyoyin fararen hula, muna ganin abune mai mahimmanci a wannan lokaci a ƙasashen larabawa da sauran ƙasashen musulmai. Abinda na ke fata kawai shine, wannan mummunan misali na ƙsar Masar, kada ya sake faruwa a wata ƙasar Larabawa, inda muke da wakilai"

Wannan matakin da ƙasar ta Masar ta ɗauka dai, ya kawo shakku bisa tabbacin wanzuwar demokraɗiyya a ƙasar Masar, wanda da farko ake fatan gani bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak.

Mawallafi: Dirk Kaufmann/ Usman Shehu Usman

Edita: Usman Shehu Usman