Shari'ar tsohon shugaban Masar
August 3, 2011A ranar Laraba aka fara shari'ar tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak a birnin alƙahira. Mubarak, wanda boren adawa da gwamnatin sa ya tilasta masa sauka daga mulki a cikin watan Fabrairu, yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma bayar da umarnin kissar masu zanga-zangar adawa da gwamnati a lokacin daya ke riƙe da muƙamin shugaban ƙasar ta Masar.
An dai ci gaba da tsare tsohon shugaban a yayin da yake kwance a gadon asibiti dake birnin Sharm el-Sheikh tun cikin watan Afrilu, amma kuma ana sanya ran zai bayyana a gaban wata kotu dake birnin alQahira, fadar gwamnatin ƙasar ta Masar. Shari'ar dai za ta gudana ne a wata makarantar bada horo ta jami'an 'yan sanda saboda dalilan tsaro, kana hukumomin sun tura sojoji da jami'an 'yan sanda dubu ukku ne domin kula da sha'anin tsaro a lokacin shari'ar.
A halin da ake ciki kuma, tashar telebijin ta Masar ta bayyana cewar tuni wani jirgin sama ya ɗauki tsohon shugaban daga Shar el-Sheikh zuwa alQahira domin shari'ar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu