1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor

June 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuJt

Yau kotun ƙasa da ƙasa mai shari´ar leffikan kissa da ke birnin Hage na ƙasar Hollande ke fara sharia´r tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, da ke zargi da hannun a cikin barkewar yaƙin basasa a ƙasar Siera-Leone.

Charles mai shekaru 59 a dunia, shine shugaban ƙasar Afrika na farko, da aka gurfanar gaban wannan kotu.

Kotun ta tuhumi Taylor da leffika ɗaya na bin ɗaya har guda 11, da su ka haɗa da hadasa fitina a Saleo da Liberia, fyaɗe, handame dukiyar ƙasa, da dai sauran su.

Kotun zata gabatar da shaidu 150, wanda za su tabbatar da wannan zargi.

Mai kare tsofan shugaban ƙasar ya ce dukkan wannan zargi ƙage ne, a ka yi masa.

A yayin da ya ke jawabi kamin fara shari´ar, shugaban kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Dunia Stefen Rapp, ya nunar da mahimmancin wannan shari´a, wajen tabbatar da adalci a dunia.