1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor

April 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3G

Yau ne a birnin Freetown, na ƙasar Sierra Leone, kotun Majalisar Ɗikin Dunia, mai shari´ar leffikan yaƙi, za ta fara sauran tsofan shugaban ƙasar Liberia, Charles taylor, a game da leffika 11, da ake tuhumar sa.

A na zargin Charles taylor, da hadassa wutar rikicin tawaye, a ƙasar Siera Leone, tsakanin shekara ta 1991, zuwa 2001, a yayin da wani ƙazamin yaƙin bassasa ya ɓarke, wanda kuma a sanadiyar sa, mutane dubu 120, su ka rasa rayuka.

Saidai, bisa dukkan alamu, shari´a tsofan shugaban ƙasar Liberia, za ta karkata, zuwa kotun ƙasa da ƙasa da ke birnin Hage kokuma La Haye, a ƙasar Holland, domin riga kafi, ga sake abkuwar wani saban rikici, kasancewar har yanzu, Charles Taylor, na da ɗimbin magoya baya a ƙasashen Liberia da sierra Leone.

Gwamnatin ƙasar Holland, ta bayana amincewar a gudanar da shari´ar a birnin the Hage kokuma La haye,amma da sharaɗin Majalisar Ɗinkin Dunia ta amince da hakan, kuma da zaran a yanke hukuncin ƙarshe, to a fidda Charles Taylor daga Holland.