1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080212 Ägypten NGOs

February 8, 2012

Takaddama a Masar game da karar kungiyoyin agaji 43 da ma'aikatar shari´a ta shigar.

https://p.dw.com/p/13zj2
ARCHIV - Die Konrad-Adenauer-Stiftung in Kairo am 30.12.2011. Ägyptische Justizbehörden gehen einem Medienbericht zufolge erneut wegen des Verdachts auf «illegale Finanzhilfen» gegen Menschenrechtler vor. Wie die staatliche Zeitung «Al-Ahram» berichtete, wird den politischen Aktivisten vorgeworfen, Gelder aus den USA erhalten zu haben. Am 29. Dezember waren Razzien bei 17 ägyptischen und ausländischen Nichtregierungsorganisationen mit dem Verdacht der illegalen ausländischen Finanzhilfe begründet worden. Betroffen war damals auch das Büro der Konrad-Adenauer-Stiftung (KAS) in Kairo. Schon im November hatte das ägyptische Justizministerium erklärt, dass viele zivilgesellschaftliche Gruppen seit dem Sturz von Husni Mubarak im Februar illegal aus dem Ausland finanziert worden seien. EPA/KHALED ELFIQI dpa 28953420
Gidauniyar Konrad-Adenauer a AlkahiraHoto: picture-alliance/dpa

Taƙaddamar da ake a ƙasar Masar game da ƙungiyoyin agaji na ƙetare ta shiga wani sabon yanayi, bayan da a ranar Litinin ma'aikatar shari'a ta Masar ta kai ƙarar ma'aikata 43 na ƙungiyoyin ƙasashen waje bisa zargin yin wasu haramtattun aikace aikace da ba a fayyace ba. Daga cikin mutanen dai har da ma'aikata biyu na gidauniyar Konrad-Adenauer ta ƙasar Jamus. Yanzu haka shugaban gidauniyar ya yi tattaki zuwa birnin Alƙahira. Tun a cikin watan Disamban bara dakarun tsaron Masar suka kai samame a ofisoshin ƙungiyoyin dake ƙasar.

Shugaban na gidauniyar Konrad-Adenauer Hans-Gert Pöttering ya je birnin Alƙahira ne domin nuna wa ma'aikatarsa zumunci. Kuma zai nemi cikakken bayani game da ainihin zargin da ake wa daraktan gidauniya da kuma wata ma'aikaciyarsu.

Ya ce: Muna ma'amala da ƙungiyoyin farar hula a nan kamar yadda muka saba tun kimanin shekaru 30 da suka wuce. Mun shirya tarukan ƙara wa juna sani akan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, ci-gaban demokraɗiyya, ci-gaban ƙasa mai aiki doka da kuma 'yanci daidai wa daida tsakanin maza da mata. Dukkan waɗannan matakai da muka saba ɗauka a Masar shekaru da yawa baya, saboda haka mun yi mamakin take-taken da mahukuntan Masar ke ɗauka a yanzu.

Kawo yanzu a dunƙule mahukuntan na Masar suka bayyana zargin da suke wa ma'aikatan ƙungiyoyin na ƙetare, wato suna tallafa wa ƙungiyoyi na siyasa da kuɗi da bawa cibiyoyin ƙetare bayyanai da ka iya yi wa Masar illa wato abin da za a iya kwatantawa da leƙen asiri.

Konferenz über Studien deutscher und ägyptischer Experten als Intiative für die ägyptische Regierung. Die Konferenz hat das Informationen und Entscheidungszentrum Ägyptens (IDSC)im Zusammenarbeit mit der Konrad-Adenauer-Stiftung in Ägypten veranstalltet. Im Foto: Dr. Hussein Elkamel und Hany Mahmoud, außenpolitische Berater, The Egyptian Cabinet Information and Decision Support Center (IDSC), Kairo, Dr. Andreas Jacobs, Leiter des Auslandsbüros der Konrad-Adenauer-Stiftung in Ägypten, Michael Bock, Botschafter der Bundesrepublik Deutschland in Ägypten, und Ashraf Hamdy, Assistent im Außenministerium Ägyptens - Das Foto hat das Informationen und Entscheidungszentrum Ägyptens (IDSC) gemacht - Kairo, 2011
Mahawara game da taimakon kungiyoyin a gaji a MasarHoto: IDSC

Pöttering ya shirya tattaunawa da ministan harkokin wajen Masar da kuma shugaban kwamitin kare haƙƙin bil Adama na majalisar dokoki. Sai dai hakan ba zai wadatar ba na cimma wani tudun dafawa, domin ba a shirya wata ganawa tsakaninsa da wakilan majalisar mulkin sojin ƙasar dake da faɗa a ji ba.

Wasu daga cikin membobin majalisar sun ƙi halartar wata tattaunawa da 'yan siyasar Amirka game da matakan kame ma'aikatan ƙungiyoyin agajin. Yanzu haka dai da yawa daga cikin 'yan siyasa a Amirka na son gwamnatin ƙasar ta dakatar da taimakon soji na dala miliyan dubu 1.3 da take bawa Masar a duk shekara, idan ba a yi watsi da zargin da ke wa ƙungiyoyin masu zaman kansu ba.

Ko shin an fake da gidauniyar Konrad-Adenauer da take zama ƙungiya guda ɗaya daga nahiyar Turai, domin ɓoye manufar ƙarar ta gwamnatin Masar cewa ƙungiyoyin Amirka kaɗai ne aka nufa? Ga dai shugaban gidauniyar Hans-Gert Pöttering.

Egyptian military stand guard as officials raid one of the non-governmental organization offices in Cairo, Egypt, Thursday, Dec. 29, 2011. Egyptian soldiers and police stormed non-governmental organization offices throughout the country on Thursday, banning employees inside from leaving while they interrogated them and searched through computer files, an activist and security official said. (Foto:Mohammed Asad/AP/dapd)
'Yan sanda sun mamaye cibiyoyin wasu kungiyoyin agaji a MasarHoto: dapd

Ya ce: Ba zan iya tabbatar da wannan ba, amma da ƙyanshi gaskiya cikin wannan zaton. Domin sauran ƙungiyoyin Jamus na ci-gaba da tafiyar da aikinsu. Shi yasa muke tambayar kanmu mai ya sa wannan matakin ya shafe mu. Saboda ba za aiya kawar da wannan zargi da ake yi ba.

Pöttering ya san cewa wannan matakin na da nasaba da siyasa. Furucin da ministar kula da ayyukan haɗin kai ta ƙasa da ƙasa ta Masar ta yi ya tabbatar da haka, inda ta ce binciken da aka yi wa ƙungiyoyin ƙetare ya tabbatar da cewa ƙasashen waje na da hannu a abubuwan tarihin da suka faru a Masar. Ministar dai ta taɓa zama cikin majalisar ministoci ƙarƙashin gwamnatin hamɓarraren shugaba Hosni Mubarak, wanda a lokacin mulkinsa ya ƙi Amirka ta tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Masar, musamman game da matakan danniya da gwamnatinsa ta yi ta ɗauka kan 'yan adawa da masu fafatukar girke demokraɗiyya a ƙasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita:Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani