Mayar da 'yan Burundi a gida daga Tanzaniya a jaridun Jamus
October 4, 2019Da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sharhin jaridun na wannan makon zai fara wadda ta yi sharhi mai taken cece-kuce kan mayar da ‘yan gundun hijirar Burundi gida daga kasar Tanzaniya. Ta ce a kwanakin baya ministan cikin gidan kasar Burundi Pascal Barandagiye ya yi nuni da cewa zaman lafiya da tsaro sun dawo a kasarsa saboda haka ‘yan kasarsa fiye da dubu 200 da ke gudun hijira a Tanzaniya za su iya komawa gida don radin kansu in kuma bukata ta kama ana iya tilasta musu komawa gida. Wadannan kalamai na ministan cikin gidan kasar Burundi kamar faduwa ce ta zo daidai da zama ga gwamnatin Tanzaniya, domin ba a jimaba kasashen biyu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda ta tanadi fara mayar da ‘yan gudun hijirar gida a farkon watan nan na Oktoba, mutum 2000 kowane mako. Sai dai a cewar jaridar har yanzu ana samun tashe-tashen hankula a Burundi musamman kai hari kan ‘yan adawa da Shugaba Pierre Nkurunziza, sannan har yanzu rigingimun da ke zama musabbabin gudun hijirar suna ci gaba da wanzuwa a Burundi.
Chin hanci da rashawa a KenyaDa take sharhi kan matsalar cin hanci da ke addabar kasar Kenya kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ruwaito wani dan jarida mai binciken kwakwaf a Kenya John Githongo da ya yi kaurin suna wajen bankado badakalar cin hanci da rashawa na cewa yaki da cin da rashawa a kasarsa ya zama wani wasa na neman suna. Zragin na dan jaridar ya zo ne yayin da gwamnatin kenya ke shan yabo bisa aiwatar da manufofi managarta don yaki da cin hanci da rashawa. Jaridar ta ce ko shakka babu Shugaba Uhuru Kenyatta ya sanya batun yaki da matsalar cin hancin a sahun gaba su kuma hukumomin shari’a na ba da himma sai dai sau da yawa ba a kammala shari’o’in da ake wa wadanda ake tuhuma da aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar. Jaridar ta ce hakan bai rasa nasaba da yadda cin hancin ya samu gindin zama a cikin hukumomin kasar.
Ebola na addabar KwangoHar yanzu batun cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na ci gaba da daukar hankalin wasu jaridun Jamus. A wannan makon jaridar Die Tageszeitung ce ta ba da labarin wani tsohon Fasto na ‘yan sanda a Kwango wato Josué Kakule da yanzu haka yake amfani da babur dinsa yana kai masu cutar Ebola cibiyoyin jinya. Jaridar ta ce shi kansi kakule da a da bai yarda cutar ta Ebola yana mata kallon almara har sai da ya kamu da ita, yanzu shi ne kann gaba wajen wayar da kan jama’a cewa cutar fa tana nan. Fasto din wanda Allah Ya yi masa gyadar dogo ya warke da cutar, amma hukumar ‘yan da ta sallame shi daga aiki, yana sadaukar da ransa, jaridar ta kwatantashi da zama daya a cikin gwarzayen da a boye suke yaki da cutar Ebola a Kwango. Da baburunshi yake jigilar masu cutar zuwa cibiyoyin jinya domin suna tsoron shiga motocin daukar marasa lafiya, haka zalika hankali bai zuwa kann babur din balantana a kai masa hari. Yana daukar kwararan matakan kare kanshi wajen jigilar masu dauke da cutar.