1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Spain da Italiya sun matsa ƙaimi kan Merkel

June 30, 2012

Taron ƙolin ƙungiyar EU a Brussels ya miƙa kai ga buƙatun ƙasashen Spain da Italiya maasu fama da matsalolin kuɗi.

https://p.dw.com/p/15OTV
Germany's Chancellor Angela Merkel talks to Italy's Prime Minister Mario Monti (R) during a European Union leaders summit in Brussels June 29, 2012. Euro zone leaders agreed on Friday to take emergency action to bring down Italy's and Spain's spiralling borrowing costs and to create a single supervisory body for euro zone banks by the end of this year, a first step towards a European banking union. REUTERS/Francois Lenoir (BELGIUM - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

Taron ƙolin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai da aka kammala ɗazu a birnin Brussels na ƙasar Belgium ya miƙa kai ga buƙatun ƙasashen dake fama da rikicin kuɗi na ƙungiyar, wato Spain da Italiya, sakamakon matsin lambar da waɗannan ƙasashe suka yi wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, inji Christoph Hasselbach wakilin DW na Turai a cikin wannan sharhi da ya rubuta.

Wani abin al'ajabi ne dagewar da ƙasashen Spain da Italiya suka yi cewa ba za su amince da yarjejeniyar tayar da komaɗar tattalin arziki, idan ba su samu taimakon rage yawan kuɗaɗen ruwa masu yawa ba. Abin nufi shi ne waɗannan ƙasashe masu fama da matsalolin da za su fi amfana da yarjejeniyar haɓaka tattalin arzikin, sun yi nasarar matsawa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lamba na yin watsi da taimakon da za ta ba su, idan ba su samu wani talafi daga wata kafa ta dabam ba.

Shugabannin gwamnatocin ƙasashen biyu wato Mariano rajoy da Mario Monti sun san cewa matsalolinsu sun shafi dukkan ƙasashen EU. Idan Spain da Italiya suka durƙushe kenan takardun kuɗin Euro sun zama tarihi.

Spain's Prime Minister Mariano Rajoy briefs journalists at a two-day European Union leaders summit in Brussels early June 29, 2012. REUTERS/Laurent Dubrule (BELGIUM - Tags: POLITICS BUSINESS)
Mariano Rajoy Firaministan ƙasar SpainHoto: REUTERS

Miƙa kai ga muhimman buƙatun Spain da Italiya

Saboda haka a dole Merkel ta saduda a wasu muhimman batutuwan. Hakan dai na da nasaba da zama tamkar saniyar ware musamman saboda adawar da sabon shugaban Faransa Francois Holland ke nuna wa alƙiblarta ta tinkarar matsalolin kuɗi. A bayan nan an jiyo Merkel na cewa muddin tana raye to ba za a ɗauki nauyin basussuka ƙasashen Turai a ƙungiyance ba, abin da ke nufin ba ta yarda da wata haɗaka ta siyasa da tattalin arziki ba.

Yaya girmar wannan saduda da Merkel ta yi? Kuma ko wannan amincewar za ta magance matsalolin dake ƙasa? Kamata yayi asusun ceto ƙasashe ya iya tallafa wa bankuna kai tsaye ba tare da sun bi ta kan ƙasashe ba. Ta haka za a hana taimakon zama ƙarin nauyi ga kasafin kuɗin ƙasashen dake karɓar taimakon. Amma da farko ya kamata a kafa wata hukuma ta bai ɗaya da za ta riƙa sa ido a kan harkokin bankuna. Sai dai lokaci zai wuce kafin kafa wannan hukuma, watakila kafin sannan Spain ba ta da sauran bankin da ya durƙushe. Hakazalika ba a san irin tsaurin ƙa'idojin da za a sanya wa bankunan ba. Saboda haka za a tsammaci wani matsin na rashin tsaurara matakan kula da bankunan. Wani batun kuma shi ne asusun ceton ka iya saye takardun lamuni na wasu ƙasashen waɗanda duk da kyakkyawan kasafin kuɗi, amma suna fama da matsalar kuɗin ruwa mai yawa ba tare da wasu ƙa'idojin tsimin kuɗi ba.

German Chancellor Angela Merkel leaves a two-day European Union leaders summit in Brussels early June 29, 2012. REUTERS/Sebastien Pirlet (BELGIUM - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: REUTERS

Kawo yanzu shugabannin ƙasashen Turai sun tabbatar da kansu a matsayin waɗanda ke iya magance matsaloli, sai dai har yanzu babu wata nasara ta a zo a gani ta magance tushen matsalolin, da suka haɗa da raunin yin gogayya a da yawa daga cikin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro da gurguwar manufar kasafin kuɗin.

Mawallafa: Christoph Hasselbach / Mohammad Nasiru Awal
Edita. Zainab Mohammed Abubakar