1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nemar wa matasa makoma

Scholz Kay-Alexander
October 3, 2019

Shin akwai kammalallen hadin kai kusan shekaru 30 ke nan da sake hade kasar Jamus? Zai yi wuya a ce haka saboda inda bangarorin biyu suka fito. Ana bukatar matasa su girma tare.

https://p.dw.com/p/3Qgt8
Tag der Deutschen Einheit 2019 | Jubiläum | Merkel in Kiel
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Rehder

Rabewar Jamus ya shafi iyalai, 'yan uwa gami da yara da ke bangarorin. Gina katangar Berlin a shekarar 1961 ya nuna wani irin salon yanayin. Galibin wadanda suka wahala lokacin mutane ne da suka manyanta da yanzu haka sun mutu ko kuma sun tsufa. Mutanen da ke nuna damuwa da samun hadin kai sun kau daga duniya ba sa cikin makomar. Ana kallon rabuwar a matsyin kuskuren da za a nemi shawo kai. Domin haka Jamusawa da ke yammaci suna nuna burin taimakon 'yan uwa na gabashi ta fannin tattalin arziki. Sun tura dubban faketin gahawa, da kayan marmari, da kayan sakawa gami da kwakoleti zuwa gabashin Jamus.

Amma harta yara da aka haifa lokacin rabuwar a tsakanin shekarun 1970 da shekaru 1980 suna ganin rayuwar a matsayin abin da aka saba. Saboda sun girma a Gamus ta Yamma ko kuma Jamus ta Gabas, sun ganin rayuwa daga bangaren da suke.

Scholz Kay-Alexander Kommentarbild App

A Yamma, a shekarar 1968 yara sun fara tamayar rawar da iyayen suka taka kan kishin kasa. Maganar cewa kasata ta fara bacewa sai maganar neman shiga sahun kasashen duniya. Tarayyar Turai ta zama kafar da za a yi amfani da ita wajen kauce wa zargin kansu bisa abin da ya faru a baya. Amma a Gabas an kafa tsarin kama karya.

An samu juyin-juya hali a shekarar 1989 sakamakon faduwar katangar Berlin, kasa da shekara guda bayan haka Jamus ta sake hadewa. Nan da nan an kawo karshen liyafar jin dadi Gabas ya sake rasa wani tasiri. Har zuwa yanzu kashi 20 cikin 100 na mutanen Yamma ba su taba ziyarar Gabas ba.

Lokacin da lamura suka sauya a juyin-juya halin shekarar 1989 an tura daruruwan milyoyin kudade daga Yamma domin gina gabashin kasar. Amma sauyin ya janyo cikin kowanne dakika guda mutum na rasa aiki a gabashi. An koma gogayyar neman aiki mai tsoka a yammacin na Jamus tsakanin bangarorin biyu. Ranar 3 ga watan Oktoban 1990 mutanen da ke rayuwa a Gabas sun raba wannan kasa sakamakon hadewa karkashin dunkulalliyar Jamus.

Deutschland Bundespräsident verleiht Verdienstorden an Alexander Gerst
Hoto: Imago Images/Eibner/U. Koch

Mutanen da suka yi rayuwa lokacin gina katanga da zamanin katangar sun sha wahala. Wannan tarihi bai bace ba amma ya wuce. Wannan dama jam'iyyar AFD masu kyamar baki ke amfani da shi abin da ya saka suka samu goyon baya. Jam'iyyar ta yi amfani da tarihin 1989 wajen samu nasara a zabuka a Jamus musamman tsakanin matasa.

Hadewar Jamus, tahirin ba zai kammala har sai abin da iyaye da kakanni suka daina magana a kai yara da jikoki sun fara maganar. Yanda aka dauki batun zai yi tasiri kan cudanya tsakanin gabashi da yammacin Jamus. Juyin-juya halin da sake hadewan Jamus ya zama lokaci na jin dadi tsakanin Jamusawa. Abin takaici ne a bar wannan labari ga bukatun siyasa. Gabashi da Yammaci Jamus ba za su sake rabuwa ba!