1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda na mulkin hadaka a Jamus

December 8, 2022

A yayin da gwamnatin hadakar Jamus ke cika shekara guda cikin sharhinsa da ya rubuta Marcel Fürstenau na tashar DW, na ganin duk da sukar da gwamnatin ke sha ta yi abin a yaba.

https://p.dw.com/p/4KgeI
Jamus | Olaf Scholz | Shugaban Gwamnati | Hadaka | Shekara Guda
Shugabn gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya cika shekara guda a karagar mulkiHoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

A ranar takwas ga watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2021 ne dai, aka kafa sabuwar gwamnati a Jamus karkashin jam'iyyun Social Democrats da The Greens da Free Democrats. A ranar 24 ga Fabarairun bana ne Rasha ta kaddamar da hari kan Ukraine, jam'iyyar Social Democrats karkashin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ya karbi mulki bayan shakaru 16 shekaru 16 na gwamnatin Angela Merkel ya sanar da kawo sauyi a majalisar dokoki ta Bundestag jim kadan bayan matakin na Rasha. Ta fuskar manufofin ketare da tsaro kuwa, Jamus ta samu tagomashi. Karuwar kashe kudi na soja a cikin tsarin kungiyar tsaro ta NATO, wata alama ce mai karfi ta aminci da hadin kai. Alamar da ke fitowa sosai daga The Greens, jam'iyyar da ke da tushen zaman lafiya wanda ta yi kira da a rushe NATO lokacin da aka kafa ta a 1980.

Marcel Fürstenau | DW
Marcel FürstenauHoto: DW

Shugaban gwamnati Olaf Scholz ya cancanci yabo saboda adawa da kiraye-kiraye, na neman karin makamai ga Ukraine. Ba za a iya cewa Jamus ba ta yi motsi ba a karkashin jagorancinsa a wannan yakin, matukar dai shugaban gwamnati da gwamnati za su hada kai da kasashen duniya matakin ya yi daidai. Idan aka zo batun yaki da zaman lafiya, sautukansa masu taushin gaske sun yi fice sosai. Ana gani daga waje ra'ayin Jamus yana da kyau ko ta yaya, rikicin siyasa kamar wadanda a halin yanzu ake fuskanta a Birtaniya da Italiya ko Sweden yana da wuya a yi tunaninsa a Berlin. Mutane da yawa a Amirka ko Brazil za su yi farin ciki, idan yanayin siyasarsu ya kasance irin na Jamusawa.