1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO Libyen Führung

March 25, 2011

A yanzu ƙasashen ƙungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika NATO sun amince da danƙa wa ƙungiyar alhakin jagorancin matakan sojan da ake ɗauka akan ƙasar Libiya.

https://p.dw.com/p/10hUu
Anders Fogh RasmussenHoto: dapd

Bayan kai ruwa-ranar da suka sha famar yi a yanzu ƙasashen ƙungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika NATO sun amince da danƙa wa ƙungiyar alhakin jagorancin matakan sojan da ake ɗauka akan ƙasar Libiya. Sai dai kuma hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake saka ayar tambaya a game da ainihin maƙasudin wannan mataki,kamar yadda wanna sharhi yayi nazari akai.

A ƙarshe dai ƙungiyar tsaron arewacin tekun Atlantika NATO ta amince ta jagoranci matakan sojan da aka gabatar domin hana shawagin jiragen saman yaƙin Libiya a samaniyar ƙasar, kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartas a makon da ya wuce. An dai daɗe ana ja-in-ja tsakanin ƙasashen ƙungiyar, lamarin da ya kusa haddasa rarrabuwar kawuna tsakaninsu. Kuma hakan a haƙiƙa tana yin nuni ne da irin saɓanin dake akwai tsakanin ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya a game da ma'ana da kuma maƙasudin wannan mataki.

Libyen Krieg Gaddafi Benghasi NATO
Hoto: dapd

Gaskiyar lamarin da ake ciki a Libiya

Da farkon fari dai an gabatar da ƙudurin na kwamitin sulhu ne da nufin kare lafiyar farar hula daga hare-haren jiragen saman yaƙin Gaddafi. Amma a halin da ake ciki yanzu matakin na fuskantar barazanar rikiɗewa zuwa wani mummunan yaƙin, wanda zai sake shafa wa ƙasashen yammaci baƙin jini a duniyar Larabawa. Tuni dai Amirka da Birtaniya da kuma Faransa suka lalata jiragen saman yaƙin Gaddafi ta yadda basu da wata barazana ga 'yan tawayen dake gabacin Libiya. Amma ɗan kama-karyar ƙasar har yau yana nan daran-daƙau akan sirdi tare da ba da umarni ga sojojinsa kuma ba shakka matsawar da sojojin ƙawancen suka ci gaba da kai farmaki kan fadar mulki ta Tripoli to kuwa ko ba daɗe-ko-bajima hare-haren nasu zai rutsa da farar hula da suka haɗa da mata da maza da kuma yara ƙanana, wanda hakan ta yi daura da maƙasudin manzancin da aka ɗora musu na ba da kariya ga farar hula. A halin da ake ciki yanzun ma dai matakan na kariya na fuskantar barazanar ɗaukar wani fasali na dabam. Domin kuwa ga alamu abin da ake so a cimma shi ne kifar da mulkin Gaddafi. Amma fa wannan ba shi ne manzancin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gabatar ba. Domin kuwa in har lamarin haka yake to kuwa wajibi ne kuma a fara karkata ga ƙasashen Yemen da Siriya, waɗanda su ma suke amfani da ƙarfin hatsi don murƙushe zanga-zangar 'yan adawa. Abin tambaya kuma shi ne: Har ya zuwa wani lokaci ne ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa zata ci gaba da ba da goyan baya ga irin waɗannan matakai idan ƙungiyar NATO ta mayar da lamarin tamkar yaƙi da Gaddafi? Mayar da jagorancin mataki zuwa hannun ƙungiyar ta NATO ba kawo wani canji ba.

A taƙaice juyin juya-halin Libiya ya shiga tsaka mai wuya, inda aka wayi gari ƙayyadadden matakin na soja ya zama nuna son kai ga wani ɓangare ɗaya dake da hannu a yaƙin basasar wata ƙasa. Duk da fatan da ake wa 'yan tawayen su cimma nasara, amma ga alamu nasararsu ita ce ta raba ƙasar gida biyu. Ta la'akari da haka ɗari-ɗarin da Jamus tayi da wannan matakin yana da ma'ana duk da ƙorafin da ake yi gamae da haka.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar