1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Kalaman Trump kalubalen Yarima Salman

Kersten Knipp
November 21, 2018

A kalaman da ya yi kan huldar dangantakar Amirka da Saudiyya, Shugaba Trump ya tabo batun Mohammed bin Salman, kalaman da za su iya zame wa shi yarima mai jiran gado ala-ka-kai, inji Kersten Knipp na tashar DW.

https://p.dw.com/p/38fSd
Riad Donald Trump Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Shugaban Amirka Donald Trump mutum ne mai furta kalamai dalla-dalla. Sai dai yana da wani salo na magana da aka gani a kalamansa na baya-bayan nan dangane da kisan dan jaridar Saudiyyan nan, Jamal Kashoggi. A ciki ya nuna shi gwarzo ne a jawabai na diflomasiya, jawabin da ya yi takatsantsan, amma yana kunshe da wani sako bayyanan ne cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya bai fi karfin doka ba.

Ga Amirka dai Saudiyya babbar aminiyarta ce a cewar Trump, wanda ba ko shaka haka ne. Amma Trump bai ce Yarima Mohammed bin Salman zai ci gaba da zama babban aminin Amirka ba. A nan Trump ya bambanta tsakanin kasar Saudiyya a halin yanzu da kuma sarkinta na gaba. A cikin kalaman na Trump akwai kuma tababa game da makomar yariman.

Mahukunta a birnin Riyadh sun karbi sakon cewa Trump ba ya goyon bayan yarima amma yana goyon bayan kasar Saudiyya, wanda haka ya sa su tunanin cewa yariman bai dace ya jagoranci kasar ba. Bugu da kari yanzu yawan masu nuna shakku bisa dacewar yariman ya karu sosai musamman tun bayan kisan Kashoggi.

Knipp Kersten Kommentarbild App
Kersten Knipp

Yariman ya tabka kurakurai na siyasa a fagen mulki ciki kuwa har da matakan sojin na rashin imani a kasar Yemen da jagorantar matakin mayar da kasar Katar saniyar ware da dora firaministan Lebanon Hariri kan mukami. Akwai kuma martanin da ya mayar wa ministar harkokin wajen Kanada a wani sakon Tweeter inda a ciki ta soki hukumomin Saudiyya da kame wata mai fafatuka 'yar Saudiyya. Yariman dai ya janye daliban kasar su kimanin dubu 16 daga Kanada. Wani mataki da ke nuna yadda mahukuntan Saudiyyar ke fatali da makomar 'yan kasarta.

Yanzu ga kalaman Trump. Shin Yariman na da masaniya kan kisan Kashoggi? Watakila ya sani ko kuma bai sani ba, inji Trump. Wannan dai ba kalamai ne na nuna zumunci wanda kuma Trump din ya san ba zai iya yi ba. Bisa ga alamu Trump dai ba zai iya sadaukar da kansa ga yariman ba.

Akwai ayar tambaya ko Sarki Salman zai iya kare dansa? A taron majalisar Ashura na ranar Litinin Sarki Salman bai fito karara ya yi maganar Kashoggi ba. Hakan dai na nufin mahukuntan Saudiyya ba su da niyyar dorawa wani shugabanta laifi.

A fili yake shirun da mahukuntan Saudiyyar ke yi ba zai hana yin tambaya game da cancantar yarima na rike mukamin siyasa ba. Fatan cewa za su iya kauce wa barazana da mayar da su saniyar ware daga kasashen duniya, ba zai yiwu ba. Hatta jaridaun kasashen Larabawa sun nuna cewa an yi bankwana da irin matakan kame baki a yi shiru, musamman tun bayan juyin juya halin da ya bazu a wasu kasashen Larabawa a shekarar 2011.