1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi game da makomar Siriya

May 29, 2012

Rikicin Siriya ya ki ci ya ki cenyewa.Rainer Sollich ya yi nazari game da makomar kasar.

https://p.dw.com/p/153va
epa03240405 A handout picture released by Syrian Arab news agency (SANA), shows Syrian president Bashar al-Assad (R) meeting with the UN international envoy Kofi Annan in Damascus, Syria, 29 May 2012. According to media reports on 29 May, French President Francois Hollande announced the expulsion of Syria's ambassador to France. The move comes in response to last week's attack bombardment of the city of Houla, in which more than 100 civilians dozens of them children died. EPA/SANA HANDOUT BEST QUALITY AVAILABLE HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Mahimman bururuka guda biyu Majalisar Dinkin Duniya ke bukatar cimma a kasar Siriya , na daya dakatar da zubar da jini sannan na biyu daukar matakan da suka wajaba, domin riga kafin abkuwar irin ta'asar dake gudana zuwa gaba.To saidai bayan kissan kiyasun da ya wakana a garin Hula inda fiye da mutane 100 suka rasa rayuka, Majalisar Dinkin Duniya ta fara yanke kaunar cimma wannan bururuka da ta saka.

A wani abu mai kama da a na magani kai na kaba,dakarun gwamnatin Siriya na cigaba da hallaka fararen hulla, kamar yadda ta faru a garin Hula inda mutane fiye da 100 da suka hada da mata da kananan yara suka rasa rayuka.Shugaban Bashar Al-assad ya sa kafa ya shure taswira zaman lafiya da Kofi Annan ya gabatar da ita duk da cewar ya rattaba mata hannu.Abin da ke daure shine yadda gamayyar kasa kasa da kasa ta kasa daukar matakan kawo karshen wannan ta'asa sai dai kawai sabbatu na fatar baka, inda ko wace kasa ke Allah wadai da abun da ya faru.

A halin yanzu kasar Siriya na shirin fadawa cikin yakin basasa. Hare-haren kan mai uwa da wabi na dakarun gwamnati ke kaiwa,maimakon ya dushe lagon 'yan adawa, sai mai ya kara masu karfin gwiwa.Hakan ya sa sun mallaki makamai da suke amfani da su domin ramuwar gayya.

A yayin da ake kare jini biri jini tsaknain bangarorin biyu, gwamnatin kasar Siriya ta shiga wani yanayi na tsaka mai wuya inda hatta yan gani kashenin Bashar Al-Assad sun yi imanin cewar da wuya gwamnati Siriya ta ci gaba da jurewa illolin mayar da ita saniyar ware da kasashen duniya su ka yi.

Demonstrators take part in a protest against Syria's President Bashar Al-Assad at Talbiseh, near Homs, May 25, 2012. REUTERS/Shaam News Network/Handout (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: REUTERS

Ga dukan alamu makullan warware wannan rikici na cikin hannuwan Kasar Rasha da ke ci gaba da daurewa Siriya gindi ido rufe.

A yayin da tsofan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ke kai gwabro da mari a Siriya, da zumar kawo karshen rikicin, shugaban kasar Amurika ya kaddamar da wani saban yunkurin diplomatiya, inda ya fara lallashi hukumomin Mosko su bada kai.

Obama ya bada shawarar a yi amfani da hanyar da aka bi wajen warware rikicin Yamel, inda Ali Abdelah Saleh ya amince ya sauka daga karagar mulki da sharadin ba za gurfanar da shi ba,dangane da lefikan a ya aikata.

Duk da cewar dai har yanzu Rasha ba ta bada cikkakar amsa ba,amma an dan samu cigaba, domin a karshen makon da ya wuce, a karon farko kasashen Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun yi magana da baki guda, inda suka yi Allah wadai da ta' sar Haula.Itama kasar Birtaniya ta yi kira ga gwamnatin Rasha ta dinga sara ta na dubin bakin gatari game da wannan al'amari.

Duk da kasahen biyu ,sun nunawa Rasha hadarin dake tattare da goyan bayan da take baiwa Siriya, wanda idan ba ta yi hatara ba, zai sanadiyar asara angizon da ta ke da shi a kasar zuwa gaba.

Syrian army soldiers and rebels sit on the top of an armored personnel carrier shortly after the Syrian soldiers defected and joined the rebels, in Khaldiyeh district, in Homs province, central Syria, Saturday May 12, 2012. Syria's uprising started in March 2011 with mostly peaceful protests inspired by successful revolts elsewhere calling for political reform. The Syrian government responded with a brutal crackdown, prompting many in the opposition to take up arms to defend themselves and attack government troops. (Foto:Fadi Zaidan/AP/dapd)
Hoto: AP

A yanzu dai kasashe gaba daya sun zuba ido su ga sakamakon rangadin Kofi Annan a kasar ta Siriya, inda ba a cimma burin dakatar da barin wuta ba, kila gamayyar kasa da kasa ta fara tunanin yin amfani da karfin tuwa, domin kifar da Bashar Al-Assad: Babu shakka wannan mataki ya na da haddarin gaske ,to amma idan cilas ta kama ta zama har cikin ido.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman