1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kommentar Äygpten

November 29, 2011

A farkon wannan shekara talakawan ƙasar sun yi nasarar ƙwatowa kansu 'yanci, sannan a wannan mako aka fara kaɗa ƙuri'a ta demokraɗiyya dake zama irinsa na farko ga mafi yawan 'yan ƙasar.

https://p.dw.com/p/13J69
Hoto: dapd

Sau biyu a wannan shekara, a cikin mamaki da girmamawa duniya ke kallon abubuwan dake wakana a ƙasar Masar. Al'umar ƙasar sun nuna wa duniya cewa a shirye suke su ɗora ƙasarsu kan tafarkin demokraɗiyya da zaɓen gwamnatin da suke so. A farkon wannan shekara sun yi nasarar ƙwatowa kansu 'yanci, sannan a wannan mako aka fara kaɗa ƙuri'a ta demokraɗiyya dake zama irinsa na farko ga mafi yawan 'yan ƙasar.

Ga mafi yawan 'yan ƙasar ta Masar wannan shi ne zaɓe na gaskiya da adalci da suka taɓa gani. Shekaru gommai suna zuwa rumfunan zaɓe amma ana juya sakamakon zaɓen, kana ana tursasa wa 'yan adawa. Shekaru 30 Hosni Mubarak ya kwashe akan mulki tare da taimakon sojoji da wani gungun jami'ai 'yan cin hanci da rashawa. Gabaninsa ƙasar ta kasance ƙarƙashin mulkin Jamal Abdel Nasser da Anwar Sadat dukkansu sojoji da suka dogara kan dakarun ƙasar. Janar-janar na sojin da suka karɓi mulki mulki bayan murabus ɗin Mubarak sun yi alƙawarin ɗora ƙasar kan turbar demokraɗiyya tare da tabbatar da tsaro da bin doka da oda. A dangane da ƙaruwar mulkin danniya an sake ta da bore a biranen Alƙahira da Iskandariya da sauran biranen ƙasar a cikin makonnin bayan nan.

Rarrabuwar kawuna tsakanin Masarawa

Ägypten Demonstration Tahir Platz November 2011
Hoto: dapd

Munanan tashe tashen hankulan kwanakin nan ya fito da irin rarrabuwar kawuna dake tsakanin 'yan ƙasar ta Masar. Yanzu haka ma dai masu zanga-zanga a dandalin Tahrir ba sa wakiltar ɗaukacin 'yan ƙasar. Fatan da yawa daga cikin Masarawa shi ne samun kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziki da kyautatuwar rayuwa. Suna adawa da sake komowar zanga-zangar da mamaye dandalin Tahrir, maimakon haka kira suke da a samu zaman lafiya da lumana. Da yawon waɗannan mutane Ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi ke magana a saboda haka ta cimma daidaito da majalisar sojin ƙasar, ta janye daga zanga-zangar. Tana fatan samun goyo baya ga wannan matsayi na ta a zaɓen na 'yan majalisar dokoki da za a kammala a cikin watan Maris na baɗi. A matsayin wadda za ta samu rinjaye a majalisar dokoki, ƙungiyar ta 'yan uwa musulmi na fatan jan akalar sabuwar ƙasar Masar.

Fargaba game da taƙaita wa mutane 'yancin walwala

Wahlen in Ägypten
Hoto: DW/A.Rahmane

Hakan ba zai yiwa masu matsanancin ra'ayin juyin juya hali daɗi ba. Dole su ji tsoron taƙaita 'yancinsu na walwala da suka daɗe suna gwagwarmayar nema amma har yanzu ba su samu ba. A dangane da manyan matsalolin da Masar ke fuskanta dole ne su yi fargaba game da samun kyautatuwar rayuwa. Dukkan waɗannan batutuwa guda biyu sun dogara da juna domin demokraɗiyya ba za ta wanzu a wurin da babu ba adalci ba.

Ƙalubalen da al'umar Masar ke fuskanta na da yawa kuma dalili ne na nuna shakku. Sai dai fara zaɓen cikin kwanciyar hankali ya ƙarfafa kyakkyawan fata. A kwanakin nan dai ana kallon abubuwan da ke wakana a Alƙahira cikin damuwa da mamaki tare da fatan Masar za ta yi nasarar shawo kan matsalolinta da ɗaukar makomarta da hannunta tare da gina ƙasa ta adalci da demokraɗiyya.

Mawallafa: Bettina Marx / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu