1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sharhi: Raunin Turai wajen tinkarar Corona

Mouhamadou Awal Balarabe
March 31, 2020

Annobar Covid-19 ta yi barna sosai a Turai da Amirka. Amma ba za su iya magance raunin da tsarin kiwon lafiyarsu ya shiga ba matikar ba su kwakware salon tafiyar da mulkinsu da ma'amalarsu da sauran kasashen duniya ba,

https://p.dw.com/p/3aFLs
DW Kommentarbild Mouhammadou Awal

Annobar corona ta zama ruwan dare saboda ta ratsa duk sassa na duniya. Amma kuma ta fi ci tamkar wutar daji a kasashen yammacin duniya, domin tana lamshe dubban rayuka a Turai da Amirka, duk da ci gaban kimiya da fasaha da suka tinkaho da shi. Babu wani mahaluki da zai iya tunanin cewar kwayar cutar Corona za ta iya gagarar Kundila a arewacin Italiya ko gabashin Faransa ko ma a Spain, ballatana ma ta iya hana asibitocin New York na Amirka katabus: Dalili kuwa shi ne: suna da asibitoci na gani a fada, suna da likitoci da suka fi shahara kuma suna da kayan aiki na zamani. Amma sai ga shi Covid-19 ta shammaci kasashen na Turai da Amirka, kuma ta nuna masu gajiyarsu a fannin kiwon lafiya.

Italien Coronavirus | Krankenhaus in Mailand
Hoto: Reuters/F. Lo Scalzo

Kasashen Turai da Amirka sun shiga cikin kanun labaru a ko'ina a duniya sobada abin fallasa da suka yi: Likitocinsu sun shiga halin gaba kura baya siyaki sakamakon karancin kayan kare kai daga kamuwa da kwayar cuta, yayin da talakawa na wasu kasashen suka rasa kayyakin gwaje-gwajen don sanin ko suna dauke da Corona koko a'a. Sannan kuma a wannan karon gwamnatocin yammacin duniya ba su yanke shawarar daukan matakan kare kasashen daga yaduwar cutar cikin gaggawa ba, duk da shaidar da yanayin da China ta shiga bayan barkewar wannan annoba. Babban abin kunyar ma shi ne rashin cudeni in cudeka tsakaninsu, inda maimakon haka, kowa ya yi ta kai ta kai gobarar bera. Godiya ta tabbata ga 'yan hakin da kasashen yammacin duniya suka raina ciki har da Cuba da Rasha da China wadanda suka kai dauki Italiya a daidai lokacin da annobar corona ta sa kowa ya juya mata baya. 

A gaskiya annobar Corona ta haifar wa tsarin rayuwar Turai da Amirka wani makeken gibi wanda cikeshi sai sun ja damara. Sun dade suna cikon baki cewa salonsu na tafiyar da harkokin mulki ba tare da rufa-rufa ba ya fi kowanne a duniya, amma kuma sai aka wayi gari kasashen da ke da matsakaicin karfi irin su Taiwan da Koriya da Kudu da Singapur da makamantansu sun sha gabansi inda suka ja wa Corona birki tun kafin ta fara barna.Salon kasashen yammacin duniya na tinkarar Covid-19 ya bambanta da karfin gwiwa da hadin kai da suka samu wajen tinkarar kalubalen yakin cacar baka a shekarun baya, lamarin da ya sa akidarsu ta yadu a ko'ina cikin duniya. Sai dai bayan da kida ya sauya, rawar ma ta kama hanyar canjawa saboda tuni abokiyar hamayyarsu a fannin kasuwani da ci gaba wato Chaina ta nuna cewa da gaske take wajen kamanta tausiya, inda take taimakawa kasashen Turai da corona ke neman kassarawa duk da cewa ba ta gama kashe wutar gabanta. 

Symbolbild Coronavirus - EU-Videogipfel
Hoto: picture-alliance/ANP

Dole ne kasashen yammacin duniya su dau darasi daga halin gaba kura baya siyaki da annobar Corona ta jefa tsarin kiwon lafiyarsu tun ma kafin komai ya lafa. Da farko dai ya kamata sun koyi kaskantar da kansu, su yi aiki kafada da kafada da sauran kasashe a duk fannoni ba wai na kiwon lafiya kadai ba saboda durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne. Sannan akwai bukatar Turai da Amirka sun san cewa bayan tiya akwai wata caca, ma'ana bayan bunkasar karfin tattakin arziki da karfin fada a ji a fannin siyasa, zamantakewa da tsarin rayuwa ma na da matikar muhimmanci a danganta tsakanin masu mulki da talakawa da kuma tsakanin kasa da kasa. Kuma su san cewa don tuwo gobe ake hanke tunkuya wato su koyi hangen nesa ta hanyar tanadin karin kayan aiki a asibitoci tun kafin annoba ta kunno kai idan ba haka ba haka ba abin da zai bambamta su da kasashe 'yan rabbana ka wadatamu a wannan fanni, kuma daularsu da tsarin rayuwarsu za su kama hanyar rushewa tamkar dai yashi. 

China Hilfe Pakistan
Hoto: Getty Images