Sharhi (Adawa): Bai kamata kasashen yamma su dauki matakan soja ba
August 28, 2013Tun bayan harin gas mai guba da aka kai a kusa da Damaskus babban birnin kasar Siriya gwamnatin Amirka ke kara matsa lamba da a kai wa Siriyar farmakin soja. Su kuwa kasashen Birtaniya, da Faransa, da Turkiya da wasu kasashen Laraba sun fi daga murya ga kiran yin kutsen sojan. Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague cewa ma ya yi ba a bukatar amincewar Majalisar Dinkin Duniya wajen daukar matakin soja a Siriya. Su kuma kasashen Saudiyya, da Qatar da kuma Turkiya kokari suke su jawo Amirka da kungiyar NATO cikin rikicin na Siriya.
Kawo yanzu Amirka na adawa da matakin sojan, bisa dalilan cewa, na farko tana da shakku game da yawan masu kaifin kishin Islama dake cikin 'yan adawar Siriya. Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta sanya sunan kungiyar Al-Nusra dake da alaka ta kurkusa da kungiyar Al-Kaida kuma ke da mayaka a Siriya, a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda. Washington na ganin cewa ba ci-gaba ne a maye gurbin hukumomin birnin Damaskus da wasu kungiyoyin 'yan tarzoma da ba a san manufarsu ba. Na biyu tana fargabar samun sakamako shigen na Iraki inda bayan katsalandan sojojin Amirka a shekarar 2003 wani rudani ya barke da ya yi sanadiyar mutuwar dubban daruruwan mutane. Na uku shi ne duk wani kutsen soja a Siriya zai haifar da mummunan rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da ma wajensa, domin bambamcin al'adu da addinai a Siriya ya bazu zuwa kasashe makwabta na yankin Golf.
Ba za a yarda da amfani da makamai masu guba
Gamaiyar kasa da kasa ba za ta amince da amfani da makamai masu guba ba ba tare da yi wani abu ba. Dole ne ta gudanar da bincike kan wannan ta'asa kana ta hukunta masu hannu a ciki. Da farko dai dole a ba wa sifetocin na Majalisar Dinkin Duniya dake bincike kan wannan batu, goyon baya. To amma 'yan siyasar kasashen yamma kamar sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague akasin haka suke yi inda suke son yin riga Malam masallaci ga sakamakon binciken. Maimakon haka kamata ya yi a gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci tare da hadin kan kasashen yamma da Rasha, da China, da kuma Iran.
A wannan makon ya kamata a gudanar da wani taron jami'an diplomasiyar Amirka da Rasha a kan shirye-shiryen taron samar da zaman lafiya a Siriya. Amma an dage wannan zaman taro bayan harin na gas mai guba. Sai dai wajibi ne a ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya ba tare da la'akari da tabarbarewar rikicin a Siriya ba. Domin muddin rikicin ya ci gaba to damar samun maslaha a siyasance tana dushewa ne.
Rikicin Siriya ya fi na Iraki da Libiya daure kai
Komin wahalar tattaunawa tsakanin shugabannin Siriya da kungiyoyin 'yan adawa don samun mafita, bai kamata Amirka da kawayenta na yamma su bari a jefa su cikin wani yaki ba. Matakan soja ba shi ne magani ba, zai kara tsananta rikici ne da janyo asarar rayukan dubban daruruwan mutane. Wajibi ne a ci gaba da kokarin diplomasiya don warware rikicin na Siriya.
Mawallafa: Mohamad Ibrahim / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdurrahmane Hassane