1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi akan tawagar sa ido ta Larabawa a Siriya

December 29, 2011

Tawagar sa ido ta ƙasashen Larabawa ta kama aikinta a Siriya. To sai dai kuma ba a sa ran cewar wannan manzancin zai haifar da wani sakamako na kirki in ji Daniel Scheschkewitz a cikin wannan sharhin da ya gabatar

https://p.dw.com/p/13bMC
Sudan's Lt. Gen. Mohamed Ahmed Mustafa Al-Dabi, the head of the Arab League monitoring mission to Syria, is pictured during a meeting in Khartoum on December 21, 2011. Launched in the hopes of ending months of unrest and quelling the regime's violent crackdown on dissent, the Arab League observer mission has been welcomed by Syria, but the opposition has been critical and called instead for the issue to be taken to the UN. AFP PHOTO / ASHRAF SHAZLY dpa (zu dpa 0985 am 27.12.2011) +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Mohamed Ahmed Mustafa Al-Dabi, shugaban tawagar sa ido ta LarabawaHoto: picture-alliance/dpa

Wakilai ɗari da hamsin daga cikin wakilai ɗari biyar da ƙungiyar haɗin kan Larabawa da tsayar da shawarar turawa zuwa Siriya domin dakatar da ta'asar take haƙƙin ɗan-Adam da kuma muzanta wa 'yan hamayya da jami'an tsaro ke yi a ƙasar, wadda take fama da wani mawuyacin hali ma kama da yaƙin basasa, tuni suka kama aikinsu. To sai dai kuma alhakin da aka ɗora wa tawagar yana da wuyan gaske, musamman ma ganin irin yaudararsu da jami'an tsaro ke yi. Domin kuwa ko da yake gwamnatin shugaba Bashar Assad ta janye tankokin yaƙinta daga garin Homs, inda zanga-zangar adawar ta fi tsanani, amma fa ba shakka an sanya su a cikin shiri a wasu wuraren dabam domin tinkarar 'yan hamayyar da zarar tawagar sa idon ta janye daga yankin.

ACHTUNG!!! THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL. TV OUT This image made from amateur video and released by Shaam News Network purports to show tear gas used on protesters in Hama, Syria, Wednesday, Dec. 28, 2011. (Foto:Shaam News Network via APTN/AP/dapd)
Ci gaban zanga-zangar 'yan adawa a SiriyaHoto: dapd

Wani abin lura dai shi ne wakilan ba su da ikon kai ziyara barikokin soja kuma a saboda haka aka tsare dukkan fursinonin siyasar da wakilan zasu sa ido wajen ganin an sake su, a ainihin barikokin sojan. Akwai ma rahotanni game da wasu matakan da ake ɗauka na canza allunan sunayen yankuna ta yadda masu sa idon ba zasu iya zuwa ainihin cibiyoyin zanga-zangar adawar ba, alhali ma dai tun da farkon fari ba wanda ya sa ran cewar manzannin ƙungiyar ta haɗin kan Larabawa zasu taɓuka wani abin a zo a gani, musamman ma ganin cewar janar Muhammed Mustafa al-Dabi daga ƙasar Sudan shi ne ke shugabancin tawagar, kuma kowa ya san irin rawar da ya taka wajen keta haƙƙin ɗan-Adam a Darfur.

Kazalika a tsakanin tawagar wakilan su ɗari da hamsin da zasu ci gaba da wanzuwa a Siriya ya zuwa ƙarshen wannan watan har da wakilai daga ƙasashen Lebanon da Iraƙi da kuma Jordan dake maƙobtaka da Siriya, waɗanda ba su ma aiwatar da matakan takunkumi na farko da ƙungiyar haɗin kan Larabawan ta ƙaƙaba wa Siriya ba. Duk da haka kuwa sai da shugaba Assad ya ƙi yarda da a tura tawagar zuwa ƙasar har sai bayan da Rasha tayi barazanar goyan bayan wani ƙuduri na Majalisar Ɗinkin Duniya domin mayar da rikicin zuwa wani matsayi na ƙasa da ƙasa, sannan ne shugaban Siriyar ya ba da kai bori ya hau.

A Syrian immigrant holds a crossed out depiction of Syrian President Bashar al-Assad during a rally against his regime in front of the Syrian embassy in Belgrade, Serbia, Friday, Dec. 23, 2011. (Foto:Darko Vojinovic/AP/dapd)
Hoton adawa da shugaba AssadHoto: dapd

Sai dai kuma duk da haka ba zai dakatar da munanan matakansa na muzanta wa 'yan hamayya ba, kamar yadda labaran kashe-kashen da ake ci gaba da samu suke nunawa. Assad dai na wata dabara ce ta jan lokaci, kuma a ƙarshe nasara ba zata danganta ne da manzancin sa ido na ƙasashen Larabawa ba, sai dai akan su kansu 'yan hamayyar wajen matsin ƙaimi a cikin gida. Wajibi ne su wayar da kan illahirin al'umar Siriya cewar kifar da gwamnatin Assad ba ya nufin kafa wani mulkin kama karya na muslmin sunni, domin wannan shi ne ainihin abin da akasarin al'umar Siriya ke fargabar afkuwarsa.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu