1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barasa ta halaka mutane 35 a Indiya

Abdul-raheem Hassan MNA
November 7, 2021

'Yan sanda a Indiya sun kama mutane 19 an kuma dakatar da wasu jami'an tsaro 9 bayan samun mutuwar mutane da dama da suka sha barasa a wasu mashaya guda uku a wata gunduma da ke jihar Bihar.

https://p.dw.com/p/42h2a
Symbolbild |  Selbstgebrannter Schnaps verursacht mind. 70 Tote in Indien
Hoto: picture-alliance/dpa/epa/P. Adhikary

Yanzu haka dai 'yan sanda a kasar ta Indiya sun kaddamar da bincike, har ma an kai ga kama mutane 19 da ake zargi da hannu a lamarin shan barasar da ya yi sandin rayukan mutane da dama, an kuma dakatar da 'yan sanda tara daga aiki.

Hukumomi a Indiya sun ce akalla mutane 1,000 na mutuwa duk shekara yawanci daga yankuna marasa galihu sakamakon shan barasar gargajiya. Ko a shekarar 1992 mutane 200 sun mutu a jihar Odisha da ke gabashin kasar ta Indiya, wasu 180 sun mace a yammacin Bengal a 2011.

Dama dai gwamnatin jihar da lamarin ya faru ta haramta sha da sayer da barasa tun gabanin zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a 2016.