1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal: 'Yan adawa sun bakaci a saki dan takararsu

February 18, 2024

'Yan adawa na Senegal sun bukaci da a gaggauta sakin dan takararsu Bassirou Diomaye Faye da ya ke tsere tun a watan Afrilun bara ba tare da ya fuskanci shari'a ba, suna masu cewa an garkame shi ne ba bisa gaskiya ba.

https://p.dw.com/p/4cYKh
Unruhe in Senegal
Hoto: Seyllou/AFP

A cikin wata sanarwa da suka fidda a ranar Lahadi 18.02.2024, 'yan adawan sun ce dole ne a samar da daidaito a tsakanin dukannin 'yan takaran da ke zawarcin kujerar shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. 

Karin bayani: Senegal: 'Yan adawa sun yi zanga-zanga cikin lumana

Kazalika 'yan adawan sun kuma bukaci da a saki madugunsu Ousman Sonko wanda aka daure a watan Yulin shekarar da ta gabata bisa yanke masa hukunci kan zargin tada zaune tsaye da hada baki wajen aikata muggan laifuka da kuma wasu tuhume-tuhume da ya musanta.

Tun bayan barkewar boren adawa da matakin dage zabe, gwamnatin Macky Sall ta sallami 'yan adawa da dama daga gidan yari da nufin kwantar da guguwar siyasar ta kada a kasar sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare wadansu.