1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal ta kama jirgin ruwa makare da 'yan ci-rani

August 27, 2024

Jirgin ruwan da ya nufi Tarayyar Turai na kunshe da mutane daga kasashen yammacin Afirka daban-daban.

https://p.dw.com/p/4jyvd
Jirgin 'yan ci-rani
Jirgin 'yan ci-raniHoto: picture-alliance/AP/Libyan Coast Guard

Kasar Senegal ta kama wani jirgin ruwa dankare da 'yan ci-rani 80 wadanda suka taso daga kasashen yammacin nahiyar Afirka a ranar Talata.

Kamen na zuwa ne sa'o'i kalilan kafun fara ziyarar Firaminstan Spain a yankin da ke funskantar karuwar 'yan ci-ranin da ke neman shiga Turai.

Senegal ta kama kwale-kwalen yan ci-rani mai shirin ketarawa

Sojojin ruwan kasar ta Senegal da ke sintiri ne suka yi kamen a kan teku mai nisan kilomita 80 daga babban birnin kasar Dakar a ranar Litinin da maraice.

Akwai mata shida da kananan yara bakwai daga cikin mutum 76 da sojin ruwan suka damke.

Sabon shugaban Senegal ya ziyarci Abuja

Fasinjojin sun hada da 'yan Senegal 55 da 'yan Guinea 11 da na Gambia bakwai da kuma 'yan Mali biyu sai kuma dan Guinea Bissau daya kamar yadda cibiyar hulda da jama'a ta sojojin kasar ta bayyana a kafar sada zumun ta X.