1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal: Kotu ta tura madugun adawa gidan yari

Binta Aliyu Zurmi
June 1, 2023

Kotu a Senegal ta wanke jagoran adawa Ousman Sonko daga zargin aikata fyade a kan wata mata da ma zargin yi mata barazana da kalaman kisa, sai dai kotun ta tura shi gidan yari na shekaru 2 bisa laifin ingiza matasa..

https://p.dw.com/p/4S4yz
Senegal Unruhen nach Urteil gegen Sonko
Hoto: Seyllou/AFP

Sonko mai shekaru 48 wanda ya kara da Shugaba Macky salla zaben da ya gabata na shirin sake kalubalantar shi a zaben shekara mai zuwa, ya musanta wannan laifi da kotu ta ce ta same shi da.

Tun kafin wannan hukunci na yau Alhamis, jagoran adawra ya ce ba komai bane illa bita da kullin siyasa da wannan gwamnatin take yi mishi da ma kokarin ganin an hana shi tsayawa takara a zaben da ke tafe.

Tuni matakin na kotu ya janyo zanga-zabga daga bangaren magoya bayan madugun adawa Ousman Sonko.