1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba mu da ruwa a rikicin Rasha da Wagner

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 29, 2023

Bayan tawayen da bai ci nasara ba da sojojin hayan Rashan na Wagner suka yi shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa, kasarsa ba ta neman a sauya gwamnati a Rasha kuma ba hannunsu a rikicin Moscow da Wagner.

https://p.dw.com/p/4TEJ2
Jamus | Shugaban Gwamnati | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Virginia Mayo/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz na wadannan kalamai ne gabanin taron kungiyar Tarayyar Turai EU da za su gudanar a Brussels, yana mai jaddada goyon bayansa ga kasashen gabashin Turai da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO. A cewarsa duk wani hari a kan kasar da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO, abu ne da ya kamata su mayar da martani na hadin gwiwa nan take.