1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus a kan Afrika

August 6, 2021

Sauyin yanayi na kara ta'azzara akidar tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel sai dai shirin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba ya la'akari da wannan matsalar.

https://p.dw.com/p/3yf9W
The Wider Image: Senegalese plant circular gardens in Green Wall defence against desert
Hoto: Zohra Bensemra/Reuters

Jaridar Der Tagesspiegel ta wallafa sharhinta mai taken "Ba'a yi nasara ba a Mali"  a kan sauyin yanayi da ke kara ta'azzara akidar tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel. 

Matsalar sauyin yanayi dai a cewar jaridar, na cigaba da yin barazana ga harkokin tsaro musamman na kasashen tarayyar Turai hanyar janyo sabani a dangantakar wakilan kasashen na EU musamman wajen kula da 'yan gudun hijira. Ya zamanto wajibi yanzu a yi nazari tare da la'akari da illar sauyin yanayi a siyasance da tattali da ma fannin zamantakewar al'umma.

The Wider Image: Senegalese plant circular gardens in Green Wall defence against desert
Hoto: Zohra Bensemra/Reuters

Karancin ruwan sha da matsanancin yanayi kamar fari da ruwan sama mai karfi na kara haifar da gagarumar gasa na mallakar filaye tsakanin al'umma. Karuwar hamada a yankin Sahel ya janyo irin wannan rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda ke janyo yaduwar kananan makamai a tsakanin mutane, kamar yadda rahoton duniya kan yanayi da tsaro ya nunar a watan Yuni.

"Babu komai a rumbun ajiyar abinci"

Da haka ne jaridar Süddeutsche Zeitung ta bude sharhin da ta rubuta kan matsananciyar yunwa da yankin Tigray ya fada. Jaridar ta cigaba da cewar abinci ya kare kuma an dakatar da tallafin da ke fitowa daga kungiyoyin agaji. 

Sudan Äthiopien Flüchtlinge
Hoto: Nariman El-Mofty/AP/picture alliance

Tuni dai abincin da hukumar bada tallafi ta Majalisar Dinkin Duniya ta kai yankin Tigray da yaki ya daidaita ya kare, ba tare da hangen sabbin da ke zuwa ba. A cewar rahotan Majalisar Dinkin Duniya, manyan motoci 20 ne suka bar filin jiragen sama da ke Semera mai makwabtaka da Tigray tun a karshen mako. Sai dai har yanzu babu tabbas ko zasu iya shigewa ta hanya mai sarkakiya mai nisan KM 300 kafin su isa inda mabukatun suke.

Domin cimma nasarar shawo kan matsalar yunwa a Tigray a kalla ana bukatar tirelolin abinci 100 a kowace rana a cewar kakakin kungiyar tallafin abinci ta duniya Tomson Phiri. Yara sama da dubu 100 ke fuskantar kamuwa da rashin lafiya saboda yunwa inji shugaban hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya watau UNICEF. A yanzu haka dai wajen mutane miliyan biyar ne ke dogaro da tallafin abinci, daga cikinsu dubu 400 na cikin matsanancin hali na yunwa.

Karancin allurar rigakafin corona a Afirka.

Malawi Impfung gegen das Corona-Virus
Hoto: Joseph Mizere/dpa/XinHua/picture alliance

A labarin ta mai taken "Zai dauki tsawon lokaci 'yan Afirka ba su samu cikkaken allurar corona ba"  Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce shirin samar da allurar shi kansa na fuskantar manyan matsaloli.

A yankin kudancin Afirka alal misali ana cikin yanayin sanyi na hunturu, kuma mafi yawan al'umma basu samu kariya daga cutar coronar ba. Ya zuwa yanzu dai kasa da kashi biyu na 'yan Afirkan ne suka samu allurar rigakafin na Covid. Nahiyar dai na dogaro ne da alluran da za ta samu daga yankin arewacin Amurka da Turai da Asiya. Kama daga rigakafin Kyanda, da tetanus da tarin fuka da kuma na Covid 19, kashi daya kacal na allurar da ake wa al'ummar ne kawai ake sarrafa su a Afirkan. 

Sai dai hakan zai sauya a yanzu. Kasashen Afirka da dama na muradin fara samar da nasu alluran rigakafin a cikin gida walau na corona ko kuma na sauran cutattuka. Kungiyar tarayyar Afirka ta ce nan da shekara ta 2040, nahiyar za ta iya sarrafa allurar rigakafi akalla kaso 60 cikin 100 na alluran da take bukata.