1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta samu sabon shugaba

Mohammad Nasiru Awal AT Bala
October 29, 2019

Rafael Grossi ya zama sabon shugaban hukumar makashin nukiliya ta duniya IAEA wanda zai gaji Yukiya Amano da ya rasu a cikin watan Yuli.

https://p.dw.com/p/3S9j4
Sabon shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi
Sabon shugaban hukumar IAEA Rafael GrossiHoto: picture-alliance/AP Photo/R. Zak

Dan kasar Ajentina Rafael Grossi, mai shekaru 58 a duniya ya zama sabon shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA. Grossi ya yi nasara a kan abokin takararsa kuma dan kasar Romaniya Cornel Feruta da rinjayen biyu bisa uku na wakilan majalisar gwamnonin hukumar ta IAEA.

Yanzu Grossi zai gaji dan kasar Japan Yukiya Amano wanda ya rasu a cikin watan Yuli da ya gabata bayan kusan shekaru 10 yana jagorantar hukumar. Grossi ya ce zai yi aiki ba da wani bambanci ba.

Ya ce: "Zan yi aiki-na wanda shi ne aiwatar da dokokin hukumar a matsayin mai zaman kanta, mai adalci wadda kuma ke a matsayi na babu ruwanta."

Hukumar ta makashin nukiliya ta kasa da kasa da ke birnin Vienna na taka muhimmiyar rawa wajen sa ido kan amfani da makamashin nukiliya ta hanyoyin lumana. Tun a shekarar 2016 take sanya ido don ganin Iran ta bi ka'idojin yarjejeniyar nukiliya da ta kulla da kasashen duniya.