1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin alƙibla a siyasar ƙasar Chadi

February 7, 2012

A 'yan makonni da suka gabata ne Chadi ta gudanar da zaben Magadan gari a karon farko cikin tarihi. Wannan na nuna alamun sauyi a fasalin siyasar ƙasar a ƙarƙashin mulkin shekaru 22 na shugaba Idriss Deby Itno.

https://p.dw.com/p/13yxK
**FILE**Chad's President Idriss Deby gestures while talking during a press conference at the EU Commission headquarters in Brussels, in a Thursday Nov. 24, 2005 file photo. Government troops using tanks and attack helicopters repelled a rebel assault on Chad's capital Thursday, April 13, 2006. President Deby assured residents he remained in control. (AP Photo/Thierry Charlier, File)
Shugaba Idriss Deby ItnoHoto: AP

Kasar Tchadi ta shiga sahun kasashen da suka kammala shinfuda demokradiya a nahiyar afrika bayan da aka gudanar da zabubukan kananan hukumomi a watan jiya wanda shine ke alamomin karshen da ke nuna wanzar da tafarkin demokradiya a cikin kasa.

Jamhuriyar Tchadi ta fuskanci alkibilar demokradiya ne a 'yan shekarun baya-bayan nan daidai da sauran kasashen afrika masu amfani da harshen Faransanci bayan taron Baule da aka yi a kasar Faransa a 1990, taron da ya kasance tamkar wata guguwar demokradiyar da ta bankado a Nahiyar ta Afrika.

Tun bayan da ya haye karagar iko a kasar shekaru 22 kenan Idriss deby Itno na zaman dan lelen wasu kasashe irinsu Faransa da ke rufe ido akan cin zarafi da kuma keta hakin bul-Adaman da ake yi a kasar a cewar Sa'ad Adoum jami'i a cibiyar nazarin siyassar kasashen yankin Afrika ta tsakiya

"Kasar Faransa misali da ke ci-gaba da nuna goyon bayanta ga Idriss Deby ta ce wai tayi hakan ne sabili da rashin nagartaccen zakara daga cikin rukunin adawa ko masu tawaye. Sauran kasashen na dari-dari ne da shi. Lallai ita Amurka na kare kasonta na man fetur,to amman bata bada karfi ga abunda ke faruwa a kasar. ita kwa kasar sin,dama dai kowa ya san fanin kasuwancinta ne kawai tasa a gaba,ba ruwanta da siyassar cikin gidan kasashe. To saidai duk da matsin lambar da wasu kasashen EU ke yi masa,kawo yanzu dai babu wani sauyin da aka gani."

A karshen watan janairun nan ne aka gudanar da zabubukan kananan hukumomi,a wani matakin da ake gani zai ja kasar ya zuwa shinfida cikkakiyar demokradiya. To saidai ba a rabu da bukar ba tunda babu wani takamaiman canji da aka samu akai bayan da kotun kolin kasar ta bayana sakamakon zabubukan inda jam'iyar MPS ta shugaba Deby ce ta lashe yawan kujerun. Sa'ad Adoum ya yi korafi akan sakamakon inda ya ce:

" Ganin yadda al'ammuran siyassar kasar Tchadi ke tafiya,ba za a saran ganin sakamakon zaben kananan hukumomin ya sha banban da na shugaban kasa da na majalissa ba,tunda tsarin siyassar Tchadi yana tafiya ne yadda gwamanti ce ke kasa komai,'yan adawa kuma basu da isashen fili,dama dai basu da kudaden yin kampe,kuma suna fama da baraka,sa'idinnan akwai matukar rashin kwarewa ga 'yan adawan."

A can baya dai jam'iyun adawa sun kauracewa zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Afrilun bara, abunda ya baiwa shugaba Deby damar zarcewa akan ikon karo na hudu biye da juna bayan da jam'iyarsa ta lashe kujeru 113 daga cikin 188 a majalisasar dokokin kasar.

Mawallafi: Issouhou Mamane Maiga
Edita: Ahmad Tijani Lawal