A cikin shirin za a ji cewar Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai na gudanar da taron koli a birnin Brussels a wani yunkuri na samo mafita ga matsalar kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai. A Najeriya an samu wani waje da matasa ke hakar zinare a kauyen Toro a jihar Bauchi. Akwai kuma shirin Tushen Afirka da Taba ka lashe.