1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya za ta gina brini marar hanyar mota

Binta Aliyu Zurmi
January 11, 2021

Kasar Saudiyya za ta gina wani katafaren birni wanda zai kasance ba shi da hanyar mota, a wani mataki na rage gurbataciyar iska da al'umma ke shaka daga sinadarin nan Carbon.

https://p.dw.com/p/3nlbS
Saudi Arabien Präsentation "The Line" in Neom Kronprinz Mohammed bin Salma
Hoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya ce za a fara gina birnin ne a watanni 4 na wannan sabuwar shekarar da muke ciki, kuma birnin zai dauki mutum miliyan guda da za su rika rayuwa a cikinsa.

Wannan sabon birnin dai zai samarwa da mutane dubu dari uku da tamanin aiki yayin da zai samar wa da kasar kudaden shiga biliyan 180 nan da shekarar 2030.

Yariman dai na kokarin karkata kasar daga dogaro da albarkatrun mai kadai zuwa wasu hanyoyin samun kudade.