1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta sassauta dokar corona a manyan masallatan kasar

Ramatu Garba Baba
October 17, 2021

A sakamakon samun raguwar masu kamuwa da cutar ne mahukuntan Saudiyya suka soma sassauta matakan kariya da aka sanya don hana yaduwar corona a kasar.

https://p.dw.com/p/41mnb
Saudi-Arabien Mekka | Erste Pilger nach Coronasperrung
Hoto: Saudi Ministry of Hajj and Umra/AFP/Getty Images

Mahukuntan Saudiyya sun sassauta matakan kariya da aka sanya a kasar don hana yaduwar cutar corona inda aka soke dokar bayar da tazara a tsakanin masallata a yayin gudanar da ibada a masallacin Makka dana Madina, duk da cewa, an nemi masu son yin ibada a masallatai, su kasance wadanda suka kammala allurar riga-kafin corona guda biyu.

Umarnin ya soma aiki daga wannan Lahadin. Mahukuntan na Saudiyya, sun dauki matakin sassauta matakan kariyar, bayan da aka sami raguwar masu kamuwa da cutar mai sarke numfashi. Mutum fiye da dubu takwas annobar corona ta kashe daga cikin sama da dubu dari biyar da suka kamu da cutar a kasar.