1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boedeker ya rasu makonni biyu da suka shige

Zainab Mohammed Abubakar
November 30, 2019

Makonni biyu da suka gabata ne dai mashahurin mai shuke-shuken Richard Boedeker ya mutu, mutumin da 'yan saudiyyan suka yiwa lakabi da sunan " Masanin shuke shuken sarakuna".

https://p.dw.com/p/3U0Y8
30.07.2011 kultur 21 Richard Bödeker 1

Mahukuntan kasar Saudi Arebiya sun sanya wa wani katafaren wurin shakatawa da ke yankin jami'an diplomasiyya a birnin Riyadh sunan wani Bajamushe da ya dauki tsawon shekaru 50 yana yiwa iyalan masarautar hidimar dasa itatuwa.

Tun daga shekara ta 1973 ne dai Boedeker ya ke tsara yadda za a alkinta yanayi na saharan Saudi Arebiya ta hanyar dasa itatuwa, mutumin da ya zartar da manyan ayyuka na dashen itatuwa a titunan Saudiyya masu cunkoso da wuraren shakatawa.