1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta ki amincewa da bukatar Amurka a game da Hamas

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv78

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta gaza samun nasarar shawo kan kasar Saudiyya domin dakatar da baiwa gwamnatin Palasdinawa taimako karkashin jagiorancin Hamas. Condoleezza Rice wadda ke ziyarar kasashen larabawa dake yankin gabas ta tsakiya ta ce Amurka na bukatar ganin kasashe sun dakatar da baiwa Hamas taimako domin ta sanya Hamas ɗin a cikin jerin kungiyoyin yan taádda. Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Saud al-Faisal yace taimakon da saudiyya ke baiwa Palasdinawa taimako ne na gudunmawar jin kai. Ƙasar ta saudiyya na baiwa hukumar gudanarwar Palasdinawa tallafi na sama da euro miliyan 40 a kowane wata. A jiya shugaban ƙasar Masar Hosni Mubarak ya shaidawa sakatariyar ta harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice cewa bai dace ba a yi hanzarin katsewa sabuwar gwamnatin ta Hamas tallafi kafi ganin kamun ludayin ta.